Ministan Albarkatun Man Fetur Zai Bayyana A Gaban Majalisa

0
531

Rabo Haladu Daga Kaduna

MINISTAN albarkatun man fetur na Najeriya, Ibe Kachikwu zai bayyana a gaban zauren majalisar dattawan domin yi wa zauren bayani kan matsalar
karancin man fetur, yasa  komai ya tsaya cik.
A ranar Litinin ne majalisar dattawa ta aike wa da ministan takardar gayyatar, bayan da ‘yan majalisar karkashin jagorancin
shugaban kwamitin harkokin man fetur, Sanata Barau Jibril suka zagaya Abuja,  domin ganin yadda matsalar man take a birnin.
Shugaba Buhari ne dai babban ministan man inda shi kuma Ibe Kachikwu shi ne
karamin ministan na man.
Da misalin karfe 2:00  ne na ranar Talata, ake sa ran ministan zai bayyana, a zauren majalisar ta dattawa. Matsalar karancin mai dai ta kwashe fiye da
watanni 10 tana addabar Najeriya kuma har yanzu an kasa shawo bakin zaren.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.