Ba’a Bar Matan Jihar Katsina A Baya Ba – Safiya Dauda

0
678

RABO HALADU DAGA KADUNA

Shugabar mata ta jamiyyar APC ta Jihar Katsina Hajiya Safiya Dauda, tajinjinawa gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, Saboda kyautatawa matan jihar.
Hajiya Safiya, ta ce gwamnatin jihar katsina ta samar da shirye shirye da dama ga daukacin matan jihar wanda zasu wajen ciyar da rayuwarsu gaba.
Shugabar ta bayyana haka ne a wata zantawa da tayi da manema labarai inda tace yanzu haka matan jihar sun fara samun tagomashi daga gwamnati kama daga koya musu sanaoi da basu tallafi da dai sauransu..
Akan hakan, ta bukaci masu rike da kujerun siyasa a fadin jihar da su koyi da gwamnan jihar wajen tallafawa alummar su wadanda suka fito suka kada musu kuru’unsu yayin zabe.
Ta kara da cewa mata suna taka rawar gani wajen zaben shugabanni na gari tana mai cewa matan jihar katsina babu abin daza cewa gwamnan jihar sai fatan alheri.
Hakazalika, ta bukaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yiwa shugaban kasa muhammadu Buhari da sauran shugabanni addua na ganin sun cimma burin na ciyar da kasa gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.