Makarantar Al-Imam Tahfizul Kur’an Ta Yaye Dalibai 52

0
902

Isah  Ahmed Daga Jos

MAKARANTAR Haddar Al’kura’ani ta Al-Imam Tahfizul Kur’an da ke garin
Saminaka a jihar Kaduna, ta yi bikin yaye dalibai mutum 9 da suka
haddace Al’kura’ani mai girma da kuma dalibai mutum 43 da suka sauke
Al’kura’ani mai girma, a garin na Saminaka.

Da yake jawabi a wajen taron Mai martaba Sarkin Lere Birgediya
Abubakar Garba Muhammad mai ritaya ya bayyana cewa babu shakka
al’ummar musulmin kasar nan,  suna da  babban kalubale a garesu kan
taimakawa  makarantun  addinin musulunci.

Ya ce  domin bama yin kokari wajen taimaka wa makarantun addinin
musulunci, mun fi mayar da hankali wajen karfafa wa makarantun boko.

Sarkin Lere wanda Tafarkin Lere Alhaji Umaru Musa Lere ya wakilta  ya
yabawa makarantar kan irin kokarin da  ta yi, a dan lokacin da aka
bude ta. Ya ce babu shakka irin kokarin da  makaranta tayi, ya nuna
cewa  nan gaba zata iya zama kowace irin babbar makaranta a kasar nan.

A nasa jawabin Shugaban hadaddiyar kungiyar makarantun Islamiyya ta
Nijeriya ta Madaris Foundation Sheikh Muhammad Idris ya ce wannan
makaranta ta zama abin koyi ga sauran makarantun islamiyya, sakamakon
irin nasarorin  da ta samu.

Ya yi kira ga daliban da aka ya ye su rike malaman  makarantar da suka
karantar da su kuma su cigaba da neman ilmi.

A nasa jawabin wani malamin addinin musulunci Sheikh Yusuf Nuhu
Dan’Alhaji ya bayyana cewa idan aka ci gaba da samun irin wadannan
makarantu a kasar nan, ba zamu yi wata fargaba ba wajen  tarbiyar
‘yayanmu. Don haka ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni  su
rika tallafa wa irin wadannan makarantu.

Tun da farko a nasa jawabin Shugaban kwamitin gudanarwa na makarantar,
Malam Nuhu Aliyu Imam Saminaka ya bayyana cewa sun shirya  taro ne don
yaye daliban  makarantar mutum 9 da suka haddace Al’kura’ani da kuma
dalibai mutum 43 da suka sauke karatun Al’kur’ani a makarantar.  Ya ce
wannan ya ye dalibai shi ne karo na farko da makarantar ta fara
gudanarwa.

Ya ce  wannan makaranta da suka bude a shekara ta 2008  tana da rassa
a garuruwan Unguwar Bawa da Sabon Birni da Juran Kari da Sigau. Kuma
yanzu  suna da dalibai sama da mutum daya

”Babban abin da muka fi mayar da hankali a kai shi ne haddar
Al’kur’ani mai girma da iya karanta shi da kuma haddace shi. Bayan
haka kuma muna koyar da darusan addinin musulunci  da boko. Babban
burinmu shi ne mu ga cewa mun gina mazaunin wannan makaranta na
dindin, a filin da muka mallaka. Don haka muna kira ga al’ummar wannan
yanki  su kara bamu  goyan baya da hadin kai, domin  mu cigaba da
kudurin da muka sanya a gaba na ilmintar da al’ummar yankin nan”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.