PDP Ta Haifar Da Ci Baya A Najeriya- Inji ‘Ya’yanta

0
447

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna

AN bayyana dimbin matsalolin da suke addabar tarayyar Najeriya musamman a fannin tattalin arziki da yake yi wa ‘yan kasa barazana da cewa, kadan ne daga cikin tarin matsalolin da PDP ta jefa kasar nan ne.

Wannan tilawar abubuwan da suka faru a bayan shekaru 16 na PDP a Najeriya na fitowa ne daga bakin ‘yan kasar da suke kishin irin halin da aka jefa ta a cikin sakamakon son zuciya.

A wata tattaunawar da suka yi da gidan rediyon muryar Amurka sashen Hausa ‘ya’yan PDP  sun bayyana cewa dole ne a yaba wa kokarin da shugaba Buhari yake yi na kokarin shawo kan matsalar Boko-Haram da sauran abubuwan ci gaban Najeriya.

Lokacin da yake hira da manema labarai, Baraden Bauci kuma tsohon sakataren shirye-shiryen jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Umaru Dahiru, ya ce “ba haka lamuran suke ba saboda, gwamnatin nan ta zo ta sami aikin zaman lafiya ta fara yinsa, kuma ga aikin gyaran tattalin arziki ga kuma aikin gyara rayuwar jama’a musammam yadda za a zauna kasa babu cin hanci da rashawa…”

Shi ma a nasa bayanin, tsohon dan majalisar Dokokin jihar Bauci, kuma dan jam’iyyar PDP Abdulmumuni Hassan Ningi, ya ce suna taya shugaba Buhari addu’a don samun nasarar kudurorin da ya sa gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.