Sace Akwatunan Zabe Ya Sa Aka Dage Zaben Cike Gurbi A Kano

0
1116

Imrana Abdullahi Kaduna

KWAMISHINAN hukumar zabe Abdullahi Adamu Kaugama,  ya bayyana batun soke zaben cike gurbin dan majalisar karamar hukumar Minjibir da cewa lamari ne da ya zamo wajibi a gudanar da shi, domin yana tattare da dimbin magudi a cikinsa.

Kwamishina Kaugama wanda hukumar ta turo daga Kaduna zuwa Jihar Kano domin gudanar da zaben ya ce lamarin ya zamo wajibi idan aka yi la’akari da irin yadda abin ya zamo tashin hankali kuma doka ta bayar da dama ga hukumar a duk lokacin da lamari ya zamo hakan a soke zaben, kuma a sake sa rana a nan gaba. Shi dai wannan lamari ya biyo bayan yadda wasu ‘yan bangar siyasa suka zo suka rika dukan jama’a suna satar akwatuna ne a lokacin da aka fara zaben. An dai dage zaben ne said illa ma sha Allahu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.