Gwanjon Tsofaffin Motocin Kananan Hukumomin Jihar Kano Ya Dace

0
412

 

Jabiru A  Hassan, Daga Kano.

AN bayyana cewa gwanjon tsofaffin motoci  na kananan hukumomi Jihar Kano 44 da gwamnatin jihar ta yi abu ne da ya dace idan aka dubi yadda tarin tsofaffin motoci suke jibge a kowace karamar hukuma ba tare da ana amfani da su ba.
Wannan tsokaci ya fito ne daga Malam Adamu Abdullahi a ganawarsa da wakilinmu, inda ya kara da cewa  wasu motocin sun dade a ajjiye tun lokaci mai tsawo wasu kuma sun yi lalacewar da ba za su sake yin amfani ba, don haka yin gwanjon su shi ne abu mafi da cewa kamar yadda Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi.
Malam  Adamu ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano ta yi tunani mai kyau, kuma duk masu sukar wannan mataki ba su yi wa al’amarin fahimta mai kyau ba shi ne ya sa suke korafin yin gwanjo motocin ba tare da sun dubi muhimmancin abin ba.
Daga karshe ya yi fatar cewa za a bai wa kowace karamar hukuma kudin da aka sayar da motocin da aka sayar mallakinta ta yadda za ta sami gudanar da wasu ayyukan ga al’ummarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.