Masu Sukar Gwamnatin Buhari Sun Manta da Abubuwan da Suka faru ne- Sardaunan Zinari

0
603

Isah Ahmed Daga Jos

WANI shugaban matasa kuma Sardaunan Zinariya  da ke  garin Jos fadar
gwamnatin jihar Filato Malam Usman Abubakar  ya bayyana cewa duk masu
sukar gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari, sun manta da miyagun
abubuwan da suka faru a baya ne, ya sanya suke wannan suka.

Malam Usman Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da
wakilinmu kan cika shekara daya da hawan gwamnatin ta Buhari kan
mulkin kasar nan.
Ya ce domin idan aka duba a baya irin halin da aka shiga a kasar nan,
duk inda  mutum  zai je hankalinsa a tashe yake. Ya ce ko masallaci
ne mutum zai je  ko coci  ko Kasuwa ko tashar mota duk hankalinsa  a
tashe yake.
Ya ce amma yanzu an sami natsuwa da zaman lafiya a kasar nan domin
dukkan abubuwan da suke sanya tsoro a cikin zuciyar jama’a sun kau.
Don haka ya ce  abin da mamaki a sami wadanda suke cewa wai gwamnatin
Buhari ta sanya al’ummar Nijeriya a cikin mawuyacin hali.
”Babu shakka daga lokacin da gwamnatin Buhari ta zo zuwa yanzu  ta yi
kokari  kan matsalar rashin tsaro a kasar nan. Yanzu an sami tsaro a
kasar nan a cikin kashi 100 an sami kashi 90. Dama babban abin da yake
damun kasar nan ke nan wato  matsalar rashin tsaro”.
Daga nan ya yi kira ga  gwamnatin ta Buhari  ta taimaka wa matasan
kasar nan ta samar masu da ayyukan yi.  Domin  matasan kasar nan su ne
kan gaba wajen jefa wa wannan gwamnati kuri’a tare da tsayawa wajen
ganin an sami nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.