‘YAN DABA SUN KASHE WANI TELA A IKKO

0
387

Daga Usman Nasidi

WANI tashin hankali ya faru a Ikorodu karshen makon nan inda ‘yan daba suka kashe wani tela kuma suka fara jifar gawarsa.
An kashe Mista Segun Showemimo,ne a shagonsa da ke Lemo,Ikorodu a ranar Asabar da rana.
‘Yan daban su kimanin 4 sanye da kaya iri daya sun far wa unguwar kan Babura 2 suna harbi sama domin tsorata jama’ a.
Wani dan uwan waanda aka kashen mai suna Marufu ya ce sun jefe shi bayan kisan , ya yi bayani : daki nan a kusa da shagon dan uwana.
Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne bayan sun harbe shi a kirji da kai ,sai suka fito da dutsuna daga cikin leda suna jifar gawarsa. Suna rawa suna zagaye gawar kafin suka tafi. Ba mu san dalilin kisansa ba , saboda mutum ne mai saukin kai.
Kakakin jami’an ‘yan sandan jihar Dolapo Badmus ta tabbatar da labarin a ranan Litini 17 ga watan Oktoba. Kuma ta ce ana gudanar da bincike cikin al’amarin. Sai dai al’umma da yawan gaske sun ce mutanen nan matsafa ne, wato ‘yan kungiyar shan jini ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.