AKALLA MUTANE 512 SUKA KAMU DA CUTAR KANJAMAU A SANSANIN JIHAR BORNO

0
352

Daga USMAN NASIDI

AKALLA mutane 512 masu cutar kwayar kanjamau a sansunan ‘yan gudun hijra a Jihar Borno inji sakataren hukumar kula da kwayar cutar Malam Barkindo Sa’idu.
Barkindo ya bayyana hakan ne a ranan Lahadi 4 ga watan Disamba a garin Maiduguri yayin da yake magana da manema labarai. Wannan abu ya tayar da hankali jama’a a fadin jihar, an gode Allah yara 2 kacal ne suka kamu da kwayar cutar.
Saidu ya ce an gano hakan ne bayan wani bincike da aka gudanar sansunan ‘yan gudun hijran a jihar.
“A yanzu haka muna gudanar da bincike a kan wadanda suka tsira ya rikicin Boko-Haram domin gano masu cutar kwayar cutar kanjamau.
“Zuwa makon da ya gabata, mun samu mutane 512, wadanda 2 daga cikinsu yara ne. A yanzu haka, kashi 2.4 cikin 100 na mutanen Jihar Borno na dauke da kwayar cutar kanjamau,wanda yake nufin mutane 108,000 bisa ga rahoton hukumar yawan mutane.
“Amma kadan daga cikinsu ne suke iya samun magani saboda yawancin ciibiyoyin magunguna na kulle. Kafin yakin Boko-Haram ya fara, muna da cibiyoyin kula guda 90 a jihar, amma guda 32 ne kacal ke aiki yanzu. Sauran na kulle saboda rikicin Boko-Haram.”
A karshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma kungiyoyin agaji da su taimaka wajen magance wannan cuta a Jihar Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.