Ya Nemi Da A Hada Karfi Waje Daya A Goya Wa Shugaban APC Na Jihar Kano Baya

0
340

Jabiru A Hassan, Daga kano.

WANI jigo a jam’iyyar APC  Alhaji Yahaya Ya’u Tinki ya yi kira ga masu hamayya da shugabancin jam’iyyar APC na Jihar Kano da su kasance masu biyayya da hukuncin da uwar jam’iyyar ta yanke na tabbatar da Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na Jihar Kano.
Ya yi  wannan tsokaci ne yayin wata zantawa da suka yi da  manema labarai, inda ya nunar da cewa samun hadin kai tsakanin bangarorin da ke adawa da shugabancin jam’iyyar ta yadda  harkokin siyasar jihar za su bunkasa kamar yadda ake bukata.
Alhaji Yahaya Tinki ya kuma yi fatan cewa nan gaba kadan jam’iyyar ta APC za ta zamo abar misali a fadin jihar domin a ci gaba da hada karfi waje guda don tafiyar da dimokuradiyya ba tare da samun baraka daga kowane bangare ba, Sannan ya yaba wa Gwamnan Jihar ta Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda ayyukan alheri da gwamnatinsa ke yi duk da rashin kudin  da ake fama da shi a kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.