Barayin Shanu Sun Mika Makamai Fiye Da 580 A Jihar Zamfara

0
321

Rabo Haladu Daga Kaduna

BATUN raba barayin shanu da makamai a jihar zamfara ya fara yin tasiri sosai.
A wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya, Birgediya-Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya fitar, ta ce barayin shanu da masu fashi da makami sun mika mugayen makamansu da dama a karshen makon da ya gabata.
Sanarwar ta ce ‘yan fashi da tubabbun barayin shanu daga garuruwan Kango da Dansadau a karamar hukumar Maru, da kuma garin Nasarawan Godel a karamar hukumar Birnin Magaji, sun mika bindigogi manya da kanana fiye da 580.
Wasu daga cikin mutanen sun fito ne daga garin Wunaka a karamar hukumar Gusau, in ji sanarwar.
Birgediya Kuka-Sheka ya ce tuni aka mika makaman ga bataliya ta 233 ta runduna ta daya ta sojin Najeriya, a gaban wasu manyan jami’an gwamnatin jihar Zamfara.
An cimma yarjejeniyar kawar da satar dabbobi a Zamfara
Sojojin Nigeria sun mamaye Zamfara
Jihar ta Zamfara dai a arewa maso-yammacin Najeriya ta dade tana fama da hare-haren yan fashi da barayin shanu.
Dubban mutane ne ake jin sun mutu a rikicin da aka kwashe fiye da shekaru biyar ana yi a sassa daban-daban na jihar.
A farkon watan Fabrairu ne aka cimma yarjejeniyar dakatar da hare-hare da kuma samun zaman lafiya tsakanin ‘yan bindigar da ke kai hare-hare kan kauyuka, da kuma ‘yan banga daga kauyukan da su ma ke kai musu hari a wasu lokutan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.