Za Mu Farfado Da Noman Rogo a Najeriya – Mista Adewumi

0
342

Jabiru   A Hassan, Daga kano.

SHUGABAN kungiyar manoman rogo na kasa Mista Adewumi ya ce  suna daukar muhimman matakai na farfado da noman rogo a kasarnan ta yadda za a kara samar da kayan sarrafawa ga masana’antun kasar nan da kuma  na kasashen waje musamman ganin cewa ana amfani da rogo wajen sarrafa kayan abnci  masu tarin yawa.

Ya yi wannan albishir ne a zantawar su da wakilin mu a filin jirgin saman kasa da kasa na  Aminu Kano, inda ya sanar da cewa Nijriya tana kashe  fiye da naira Miliyan dari takwas wajen shigowa da shi cikin kasarnan, wanda akwar bukatar ganin cewa an inganta noman sa  saboda amfanin ga  al’umma da kuma masana’antun da ake da su a ciki da wajen kasar nan.

Mista Adewumi ya kara da cewa  kungiyar su tana kokarin  gabatar wa da gwamnonin arewacin kasar nan  wasu manufofi kan noman rogo tare da nuna bukatar shigar da noman rogo cikin shirye-shiryen su kamar yadda ake  bunkasa shirin noman shinkafa da alkama da kuma tumatur, wanda a cewarsa, shigar da noman rogo ciin shirin gwamnati na wadata kasa da abinci zai kawo bunkasar tattalin arzikin kasa da bude gurabe na dogaro da kai.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnan jihar kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan Jihar Katsina  Alhaji  Aminu Bello masari da sauran gwamnonin arewacin kasar nan dasu  shigar da noman rogo cikin shirye-shiryen su  na bunkasa noma  domin kara inganta tattalin arzikin jihohin su da kuma kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.