‘Yan Kasuwa Na Jin Dadin Karyewar Farashin Dala A Nijeriya-Sani Sulaiman Saminaka

0
460
Isah Ahmed, Jos
WANI dan kasuwa da yake sayar da kayayyakin wuta a yankin Saminaka da
ke Jihar Kaduna kuma yake fita kasashen waje don sayo kayayyaki Alhaji
Muhammad Sani Sulaiman Saminaka ya bayyana cewa babu shakka  ‘yan
kasuwa sun ji dadin matakin da gwamnatin Nijeriya ta dauka na karya
farashin Dala a Nijeriya. Alhaji Muhammad Sani Sulaiman Saminaka ya
bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce ‘yan kasuwa sun ji dadin wannan al’amari na karyewar farashin
dala a Nijeriya, domin ada suna cikin fargaba na hauhawar tashin
farashin wannan dala.
Ya ce  ada dan kasuwar da yake da jari kashi 100 ya koma kashi 50
sakamakon tashin wannan farashin dala. Kuma  kamar ‘yan kasuwar da
suke fita su sayo kaya  kwantena guda a waje, jarinsu ya koma kaya
rabin kwantena sakamakon wannan tashin Dala.
Alhaji Sani Sulaiman ya yi bayanin cewa faduwar Dala a kasar nan, zai
sa a sami saukin kayayyaki. Domin duk hauhawar farashin kayayyaki  ya
taso ne sakamakon tashin farashin Dala. Idan ‘yan kasuwa suka sami
Dalar nan a cikin sauki  suka sayo kaya za su  rage farashin kayan.
”Hauhawar farashin Dalar nan  ne yake sa ‘yan kasuwa su rike
kayayyakin da suke sayowa daga kasashen waje. Don suna tunanin cewa
farashin Dalar nan zai ci gaba da tashi, amma da zarar sun ji cewa
farashin Dalar nan yana faduwa, dole za su fitar da kayayyakin da suka
sayo su sayar. Don haka lokacin da farashin Dalar nan yake hauhawa a
rana daya sai farashin kaya ya tashi har sau uku”.
Ya ce don haka yanzu da farashin Dalar nan ya karye farashin
kayayyaki ya fara saukowa a Nijeriya. Don haka mu ‘yan kasuwa mun yi
mutakar farin ciki da wannan al’amari na karyewar farashin Dala a
Nijeriya.
Ya ce babu shakka wannan samar da dala ga bankunan Nijeriya da
gwamnati ta yi yana da matukar alfanu kwarai da gaske ga mutanen
Nijeriya. Domin duk wannan matsi na rayuwa da aka shiga a Nijeriya zai
yi sauki.
Ya yi  kira ga gwamnati ta ci gaba da baiwa bankunan kasar nan wannan
Dala, domin  ta yawaita a bankuna, idan ta yawai dole ne za ta yi
sauki. Saboda bankunan  zasu a rika yin gasa, kowa zai so ya sayar da
tasa Dalar. Kuma suma ‘yan kasuwa za su shiga yin gasa wajen yin sauki
kan kayayyakin da suke sayarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.