GWAMNAN JIHAR BINUWAI YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA

0
394
Daga Usman Nasidi
GWAMNAN jihar Binuwai ya tsallake rijiya da baya a kan hanyarsa ta dawowa daga garin Zaki biam inda wata motar haya ta kusa cikin motarsa.
Wannan Abu ya faru ne a ranar talatar nan yayin da yake hanyar dawowa daga ziyarar inda ‘yan bindiga suka kai hari kasuwan doya a jihar wanda akalla mutane 32 suka rasa rayukansu.
Duk da cewan babu wanda ya rasa rayuwarsa a hadarin motar, daya daga cikin fasinjojin ya samu rauni a kansa kuma an kai shi asibiti. kana kuma, Comrade Kris Atsaka, wanda shi ne shugaban kungiyar ‘yan jaridan jihar ya jikkata.
A cewar jama’a, ‘yan bindigar sun kashe akalla mutum 32 a Zaki Biam din, sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Moses Yamu ya ce mutum 17 ne suka mutu yayin da wasu 11 suka jikkata.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin, ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga ‘yan uwan wadanda harin ya shafa.
Mai magana da yawun shugaban Femi Adesina, ya ce: “Shugaba Buhari ya umarci jami’an tsaro su fara binciken gaggawa da nufin hukunta wadanda suka aikata laifin.”
Moses Yamu ya shaida wa majiyarmu cewa: “Da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Litinin ne wasu mutane a cikin mota da kuma wasu a kan babura suka shiga garin kuma suka bude wa wasu ‘yan kasuwa wuta.”
Ya kara da cewa tuni an kara tsaurara matakan tsaro a yankin kuma tuni aka kama mutum uku wadanda ake zargin suna da hannu a harin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.