Wani Matashi Ya Fadi Matacce Yayin Da Yake Tone Kabarin Wata Dattijuwa

0
330

MUSA MUHD.KUTAMA, Daga  Kalaba

WANI matashi mai suna Ifeanyi Nwafor  ya mutu nan take a Onunwankwo da ke yankin Umuhuali, karamar hukumar Ishielu jihar Ebonyi  loakcin da yake kokarin tone kabarin wata dattijiwa da ta dade da mutuwa aka binne ta.

Shugaban kungiyar  matasan kauyen . Nonso Ekuma, da yake yi wa manema labarai karin haske game da yadda matashi dan shekara 29 da haihuwa Nwafor ya mutu ya ce “matashin ya halarci bikin kwanan zaune da aka yi da za a binne mamaciyar washegari dattijuwar mai suna Ajioku Mgbanya an binneta da kayan kyala-kyalai kila abin da ya dauki hankalinsa ke nan ya tafi ya tone ya kwashe .

Sai ma da aka gama aka samu wasu lokuta masu tsawon gaske daga bisani yaron ya koma ya tone gawar domin ya kwashe kayan da aka binne ta da su yana cikin yin haka kamin ya gama hakarsa ta cimma ruwa ne ya yanken jiki ya fadi matacce”in ji shugaban matasan

Ko yaya aka yi ma aka ga gawar mamacin da ke tonon kabarin, shugaban kungiyar matasan ya ci gaba da cewa “ai dama yana cikin hakar kabarin ne digar da yake hakar da ita ta kafe a ciki shi kuma ya yanke jiki ya fadi aka zo aka tarar da gawarsa kwance a bakin kabarin inda yake hakar kabarin matar”.

Wakilinmu ya tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi . Jude Madu,game da wannan labari ya ce hakika labarin hakan ya zo masu amma fa suna nan suna gudanar da bincike duk  yadda ta kaya zai bara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.