MUTANE 290,000 SUKA YI RAJISTA DA SHIRIN N-POWER CIKIN KWANAKI 3

0
246
Daga Usman Nasidi
AKALLA sama da mutane 290,000 suka yi rajista a shafin yanar gizo na shirin samar da aikin gwamnatin tarayya na N-power.
Babban mai taimaka wa shugaban kasa kan samar da ayyukan yi, Afolabi Imoukhuede, ya bada wannan bayanin lokacin da yake ganawa da wadanda suka amfana da shirin a Benin babban birnin jihar Edo.
A cewarsa mutane 200,000 ne da suka gama makaranta suka shiga cikin kason farko na shirin yayin da za a kara daukar mutane dubu 300,000 a kaso na biyu.
Majiyarmu ta samu labarin cewa ya kuma koka kan yadda ake shigar da bayanai ba daidai ba yayin da matasan suke shigar da bayanansu a shafin yanar gizon.
Imoukhuede ya ce gwamnati tana kashe Naira Biliyan 6 a duk wata wajen biyan mutanen da suke karkashin shirin inda ya ce wannan ba karamin kudi ba ne.
Ya kara da cewa a wannan karon za a fi bada fifiko ga mutanen da suke zaune a karkara domin maganin kwararowar mutane cikin birane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.