Bayan Ya Shafe Shekaru 29 A Gidan Kasu Ya Nemi Da A Tallafa Masu Da Sauri

0
216

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

IBRAHIM Abdullahi Katsina shi ma direba ne dan asalin garin Runka  da ke karamar hukumar Dutsin-ma yanzu kuma a karamar hukumar Safana  ya shafe shekara 29 a kurkuku shi ma, shi kuma sanadin kayan sumoga da ya dauka, wasu suka kirawo shi suka dora masa a mota; ya yi wa wakilinmu na kudanci a Kalaba  bayanin yadda tasa kaddarar ta same shi.

“Ni mazaunin Fatakwal ne sai na samu matsala na dawo Akwa Ibom da ma ina da mota pick-up aka kama ni ranar 19-5-1988 sojoji biyu las kofur Idris Kanya da kofur Ndarake Ufot da kuma wasu farar hula biyu Emmanuel Akpan da Dann Okeke suka kira ni suka yi shatar motata zan kai masu kaya zuwa Aba jihar Abiya suka ba ni kayan aka loda a mararrabar Itam wato Itam Junction kayan sun kunshi atamfofi da kayan shafe-shafe babu rasidi na kayan amma suka ce ga inda zan kai kayan tsakanin Ikot Msen  sai ‘yan sanda suka tare mu suka nemi takardun kaya babu sai suka dawo da mu Uyo aka yi bincike aka gano ashe kaya na wani jami’in kwastan ne daga nan aka kulle mu na tsawon wata daya, daga nan aka kai mu kotu mai daraja ta 1. Daga nan aka kaimu gidan yari na Uyo na zauna a kurkukun na tsawon wata 13. Ina jiran hukunci “.

Ya ci gaba da cewa daga nan kuma “sai aka kai mu kotun soja da ke hukunta wadanda aka kama da laifin makamai aka dage zaman a wannna rana, washegari muka koma daga nan  mu uku aka yanke mana hukuncin daurin rai-da-rai, yanke mana wancan hukunci ne sai Barista Ita Enang ya ce shi bai yarda da hukuncin da aka yanke mana ba an daure mu ba bisa ka’ida ba ina laifin a ce daurin wata uku lokacin gwamnan soja Godwin Abeh mulkin soja ne an yanke min wancan hukunci ne a 1990 daga nan aka dauke ni aka kai Ikot Ekpene kurkuku ni da Emmanuel Abang. A 1993 aka dauke ni aka mayar da ni zuwa Uyo sai aka sake dauke ni a 1994 aka mayar da ni Fatakwal haka kuma a 23-11-2001 aka dawo da ni uyo ,shekara ta 2004 aka sake mayar da ni Ikot Ekpene sai a 12-10-2014  aka mayar da ni kurkukun Ogoja da ke nan Kuros Riba;  daga can a shekara ta 2015 aka dawo da ni Afokang ,kurkukun Kalaba sai a ranar 9-6-2017 aka sake ni”inji shi.

Ko wace sana’a ko darasi zaman ya koya maka “Na koyi sana’ar walda da dinki da kuma na yi noma ma a kurkuku ni manomi ne “.sakona ga gwamnati da sauran al’umma shi ne idan mutum ya fito daga kurkuku kamar yadda na fito kamata ya yi gwamnati ta sanya ido a kanmu ta ba mu wani tallafi domin mu samu abin yi, sai dai kuma ina so gwamnati ta sani cewa kurkuku fa cike yake da cin hanci da rashawa yau idan ba kana da wanda zai tsaya maka ko gata na kurkuku na shan wahala cututtuka na kama na kurkuku wasu da yawa saboda haka da kuma yunwa sun mutu suma ma’aikatan gidan yarin suna take hakkin na tsare idan gwamantin tarayya  ta aiko da abinci a raba mana  suna sayarwa.

Zan so a dawo da kungiyoyin sa- kai da suke taimaka wa na kurkuku su ci gaba da yi, kudi am lokacin da Obasanjo ya yi mulki aka ce a yi mana intabiyu a ba kowane lauya Naira Dubu 500 don a fitar da mu sun kasha kudin ba su biya su lauyoyin ba. Haka kuma kudade da ake turowa daga waje don kyautata wa na kurkuku duk handamewa suke yi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.