Kano Pillars FC Ta Kai Wa Sarkin Hausawan Kalaba Da Magoya Bayansu Ziyara

0
206

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga  kalaba

RANAR Litinin ta wannan mako ne shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars suka kai wa mai girma sarkin Hausawan Kalaba Alhaji Salisu Abba Lawan a fadarsa karkashin jagorancin babban manajan tim din  Alhaji Salisu Yaro “Maigida” a jawabin da ya yi na dalilin da ya sa suka kawo ziyarar, ya ce “domin neman tubarrakin manya da kuma addu’arsu ya sanya bayan  mun gama wasa da kungiyar kwallon kafa ta ne muka yanke shawarar kawo maka ziyarar ban girma.

Alhaji Yaro ya kara da bayyana matukar farin cikinsu na ganin yadda al’ummar arewacin Nijeriya suke zaune lafiya a Kalaba da sauran sassan jihar kana kuma ziyarace ta kara dankon zumunta tsakaninmu .

Da yake jawabi marhabun lale da bakin nasa Alhaji Salisu Abba Lawan ya nuna matukar farin ciki da ziyarar tasu ya ce “ina mai matukar farin ciki da kuka kawo min wannan ziyara Allah ya saka da alheri kuma kamar yadda kuka zo nan Kalaba lafiya Allah ya mayar da ku gida lafiya.Kuma ina addu’ar Allah  ya kara daukaka kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da ci gabanta..

Bayan da bakin suka fito daga gaisar da Sarkin Hausawan sai ‘yan wasan suka rika yin hotuna da magoya bayansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.