Ruruta Rikicin Makiyaya: Yarfen Siyasa Ce Ake Yi Wa Shugaba Buhari- Mai Aliyu

0
161
Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
SHUGABAN kungiyar makiyaya (Miyetti Allah) na kasa reshen jahohin
arewa maso gabas Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ya kalubalanci mutanen
da ke kara rura wutar rikicin makiyaya da al’ummar kudancin kasar nan
da cewar suna yin hakan ne  a kokarinsu na rufe Bunsuru da fatar Kura
don yi wa gwamnatin Muhammadu Buhari yarfen siyasa don ya fito daga
tsatson Fulani.
Shugaban kungiyar makiyayan ya bayyana hakan a cikin tattaunawarsa da
GTK a garin Damaturu kan hare-haren da ake kaiwa wassu yankuna a
kudancin kasar nan tare  yin garkuwa da mutane don biyan kudin fansa
ake kuma danganta aikata hakan kai tsaye ga Fulani makiyaya.
Mai Aliiyu ya kara da cewar, abin da masu wannan zarge-zarge kan cewar
Fulani makiyaya kada’an ne ke aikata irin wannan ta’assa suka manta
shi ne, ai kafin zuwan wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ana samun
irin wadannan hare-hare jifa-jifa wani lokacin tsakanin makiya Fulani
da manoma wani lokacin kuma tsakanin Fulani makiyayan da wasu kabilu
ko kuma barayin shanu wadda  aksari za ka tarar da anfi cutar da
makiyayan domin kuwa haka siddan ake bin su daji da wuraren kiwonsu
ana kashesu tare da yin awon gaba da dabbobinsu, amma su makiyaya ba su
taba dora alhakin hakan ba ga gwamnatin tsohon shugaba Jonathan ba.
Don haka sai ya gargadi masu kara rura wutar wannan rikici da zimmar
bata sunan gwamnatin Muhammadu Buhari a siyasance da su kwana da sanin
cewar tuni fa mafi yawan al’ummar Nijeriya sun san ba hakan ba ne
lamarin illa dai sun san da cewar, wasu ne ke shigar burtu hade da
mugayen iri cikin ‘ya’yanmu na makiyaya ake amfani da su wajen aikata
irin wannan ta’asa ta yawaitar hare-hare da yin garkuwa da mutane don
karbar kudin fansa.
Ya ci gaba da cewar, ba wai ya na cewar, ba a samun kai hare-hare
a bangaren makiyaya bane lalle akan samu amma hakan ma takan kasance
ne idan har an takale su ko kuma an sace musu dabbobinsu an kuwa sani
cewar shi makiyayi kuwa dabbobinsa sune abokan rayuwarsu. Har ila yau
aduk al’umma akan samu bata gari, don haka a mafi yawa-yawan lokaci bata-garin
matasanmu na makiyaya su ma sukan kai harin daukar fansa amma ba wai
komai a ce  makiyayan ne ke da alhakin hakan ba balle ma a ce wai har
kungiyar kan gayyato Fulani daga wasu kasashe irin su Mali, Jumhuriyar
Nijar, Senegal da sauransu wai don aikata ta’addanci a cikin kasar mu Nijeriya cewar,
wannan abu ne da ba zai taba yiwuwa ba.
Daga nan sai shugaban ya shawarci matasa ‘yan kabilar Ibo da na yankin
Naija Delta musamman da ma na wasu bangarorin kasar nan da su kai
zuciya nesa bisa maganganunsu na tada zaune-tsaye hakan ba komai ba ne
sai kara rura wutar kiyayya a tsakanin ‘yan kasa inda shugaban ya ba da
misali da kalaman matasa ‘yan kabilar Ibo da suka yi a baya mai
cewar,wai sun bada wani takamammen lokacin da suke neman makiyaya
Fulani a kan su gaggauta barin yankin in kuwa ba haka ba su gamu da
fushinsu, a cewarsa hakan ba ita ce mafita ba, domin kuwa Fulani ma
‘yan kasa ne kamar kowa wadanda kan iya shiga kowane yanki na kasar
nan su sakata su wala kamar yadda tsarrin mulkin kasar nan na shekara
ta 1999 ya yi tanadi.
Alhaji Mai Aliyu ya kuma roki ita kanta gwamnatin tarayya da ta dauki
matakin gaggawa kan wannan lamari domin kuwa yin sakaci da gwamnatocin
baya ke yi shi ya haifar da halin da ake ciki a yanzu. Kana ya gargadi
mambobin kungiyarsu ta makiyaya da su guji daukar doka a hannunsu
domin mai kaza a aljihu baya jimirin as. Kana ya kuma nemi gwamnatin
tarayya da ta hanzarta daukar matakin gaggawa kan irin yadda al’ummar
Tsaunin Mambila suka aiwatar da kisan gilla akan makiyaya haka siddan
ta yadda suka hallaka makiyaya bila-adadan tare da kashe dabbobi
masu tarin yawa, tun kafin lamarin ya canza salo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.