Home Labarai An Kama ‘Yan Kasar China Da Na Najeriya Kan Hakar

An Kama ‘Yan Kasar China Da Na Najeriya Kan Hakar

0
176

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN tarayya ta bada umarnin a kama shugaban kamfanin Solid Units
Alhaji Abdullahi “Dan China.”
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanini da suke hakar ma’adinai a jahar Flato ba tare da izini ba, kuma ta ayyana shugaban da ya daga cikin kamfanoni da suke aiki a wuri da ake kira Zirak, a zaman wanda take nema ruwa a jallo.
An kama ‘yan kasar China 8 ciki harda wasu ‘yan Najeriya.
Ministan ma’adinai Kayode Fayemi, wanda mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Babagana Mungono ya rufawa baya, yace ya ayyana aiki da dokar hakar ma’adinai ta Najeriya ta shekara ta 2007, wajen dakatar da aikace-aikcen kamfanonin
hakar ma’adinai da kamfanonin Solid Units da kuma Jotex a jahar Flato.
Minista Kayode ya ce, gwamnatin tarayya tana neman Alhaji Abdullahi Adamu Usman, mai inkiya dan China ruwa a jallo, shi ne shugaban kamfanin Solid Units, wadanda suke aiki ba tare da izini ba.
Da yake magana, Gwamnan jahar Flato Simon Lalong, ya bayyana farin cikinsa kan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka.
Mazauna yankin sun bayyana jin dadinsu na daukar wannan mataki da fatar gwamnatin tarayya za ta samar musu da kayan more rayuwa. Kamfanonin suna ta kwasar arzikin Najeriya ba tare da samar wa mazauna yankin kayan more rayuwa da kuma ayyukan
yi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Login

Lost your password?
%d bloggers like this: