KOTU TA YI WATSI DA KARAR DA JANG YA KAI GWAMNATIN FILATO

0
172

 Isah  Ahmed, Jos

Babbar kotun jihar Filato da mai shari’a Pius Damulak ke shugabanta tayi da watsi da karar da tsohon gwamnan jihar  kuma Sanata mai wakiltar mazabar Filato ta arewa Sanata Jonah Jang ya kai gwamnatin jihar  kan bayyana sakamakon hukumar binciken gwamnatinsa da gwamnatin ta jihar  ta kafa a shekarar da ta gabata.

Tun da farko dai a shekarar da ta gabata gwamnatin ta jihar Filato, karkashin gwamnan jihar Simon Lalong ta kafa wata hukumar bincike kan yadda tsohuwar gwamnatin ta Jnag ta kashe kedaden jihar tun daga shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2015.Bayan da wannan hukuma ta kammala bincikenta ta mikawa gwamnatin jihar, sai  tsohon gwamnan  Sanata Jonah Jang ya shigar da kara gaban wannan kotun.  A inda ya roki kotun ta hana gwamnatin jihar ta fitar da sakamakon rahoton wannan hukuma ko kuma amfani da rahoton hukumar. 

Da yake yanke hukumcin mai shari’a Damulak ya bayyana cewa  doka ta baiwa gwamann jihar Simon Lalong ikon binciken dukkan wata ma’aikata ko kuma wata hukuma dake jihar. Don haka kafa wannan hukuma da ya yi bai sabawa doka.

Har’ila yau ya ce a cikin rahoton binciken wannan hukuma babu inda aka ce ga wajen da mai karar ya yi laifi. Don haka ya yi watsi da wannan kara. Kuma ya umarci mai karar ya baiwa gwamnan jihar Simon Lalong naira dubu 400  kuma ya  baiwa gwamnatin jihar da Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Barista Jonathan Mawuyau naira miliyan 1 a matsayin diya. A zaman kotun dai mai karar Sanata Jonah Jang da lauyinsa ba su sami halartar  ba. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.