HUKUMAR SAURARON KARARRAKIN JAMA’A TA FILATO TA SAMI NASARAR DAIDAITA KARARRAKI 231-ABDULLAHI MUSA  

0
176

 Isah  Ahmed, Jos 

ALHAJI Abdullahi Musa shi ne Danburan din garin Nyalun kuma  kwamishinan sauraron kararrakin jama’a na Jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana ayyukan wannan hukuma kuma ya bayyana cewa a ckin shekaru biyu sun sami nasarar daidaita kararrakin jama’a guda 237, batare da karbar ko kwabo ba. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

GTK: A wanne lokaci ne aka kafa wannan hukuma ta sauraron kararrakin jama’a kuma mene ne ayyukanta?

Abdullahi Musa: To ita dai  wannan hukuma an kafa ta ne a shekarar 1978, wato lokacin mulkin soja a matakin tarayya. Kuma  hedkwatar wannan hukuma tana zaune a babban birnin tarayya Abuja. Tun daga  lokacin da aka kafa  wannan hukuma,  aka bude rassanta a dukkan jihohin Nijeriya.

Bayan haka ba wai a Nijeriya kadai ake da wannan hukuma ba. A kowace kasa ta duniya akwai wannan hukuma domin ayyukanta yana da matukar mahimmanci. Kuma ayyukan wanann hukuma sun shafi  aikata ayyuka  daidai, wanda ya shafi ayyukan gwamnati ko kamfani ko  tsakanin al’umma da dai sauransu.

Wato abin nufi a nan, shi ne idan misali gwamnati tana aikata ayyukan da ba daidai ba wadanda al’umma ba sa jin dadi, kuma sun saba wa dokokin Nijeriya. Wannan hukuma tana da damar ta shiga ciki ko an rubuto mata ko ba a rubuto mata ba. Za ta shiga cikin irin wannan al’amari ta yi magana a daidaita irin wadannan abubuwa.

Haka kuma misali  idan mutum ma’aikatacin karamar hukuma  ne ko  jiha  ko tarayya  aka dakatar da shi, ko aka kore shi ba bisa ka’ida ba, idan ka rubuto mana aikin wannan hukuma ne ta karbi takardar da ka rubuto mana ta tura ma’aikacinmu zuwa wannan ma’aikata da ka kawo mana kara ya binciki gaskiyar maganar. Idan muka gano cewa korar da aka yi ma’aikacin  ko kuma dakatarwar da aka yi masa, an yi ne ba bisa ka‘ida ba za mu sanya wannan ma’aikata ta mayar da shi bisa aikinsa. Idan kuma abin da aka yi an yi ne bisa ka’ida za mu fada masa.

Idan muka koma bangaren kamfanoni idan aka kori wani ma’aikaci ba bisa ka’ida ba ko kuma an danne masa hakkinsa an kasa biyinsa, idan ma’aikaci ya rubuta mana ya kawo za mu bi wannan kamfani mu binciki gaskiyar maganar, idan muka gano ma’aikaci yana da gaskiya za mu sanya kamfani ya biya shi hakkinsa. Idan kuma ma’aikaci yana da wata damu da wani kamfani da yake yi wa aiki, idan ya kawo mana za mu kira kamfanin mu kira ma’aikacin mu zauna mu binciki maganar mu gano mai gaskiya mu bai wa mai gaskiya gaskiyarsa.

Haka nan kuma a tsakanin al’umma idan suna da wata damuwa a tsakaninsu. Misali idan mutum biyu suka sami damuwa kan wani fili kowa yana cewa nasa ne. Idan aka kawo mana maganar za mu shiga maganar mu gano mai gaskiya, domin a ba shi gaskiyarsa. Kadan kenan daga  cikin ayyukan da muke gudanarwa.

GTK:  Ganin irin koke-koken da ake yi a kasar nan, kan lalacewar harkokin shari’a shin idan aka kawo maku kara ana samun nasara kuwa?

Abdullahi Musa:  Kwarai da gaske idan mutane suka kawo mana kara suna samun nasara. Gaskiyar magana wannan hukuma ta sauraron kararrakin jama’a kuma  tana taimakon marasa hali. Domin misali idan ka kai karar wani kan wani abu da ya faru tsakaninku, idan ka kai kotu kaga watakila dole ka dauki lauya, za ka biya lauyan nan da ka dauka. Kuma wannan kara da ka kai za ta iya yiwuwa ta dauki tsawon shekaru ba a yanke hukumci ba. Za ka yi ta kashe kudi, amma idan ka kawo kara wannan hukuma za mu sasanta wannan magana, kuma za mu sanya abi abin da doka ta ce.

Kuma a  aikin da muke yi ba ma karbar ko kwabo na wanda ya kawo mana kara. Hakkin wannan hukuma ne ta dauki nauyin dukkan binciken da za ta yi a ko’ina ne ba tare da ta karbi ko kwabo, daga wanda ya kawo kara ba.  Duk inda za mu je ba za mu karbi ko kwabo ba, hakkinmu ne mu tura ma’aikatanmu zuwa ko’ina su je su binciki karar da aka kawo. Misali koda kana bin wani ne bashi idan muka bi maka muka sanya aka biyaka wannan bashi, ba mu bukatar ka ba mu ko kwabonka kan wannan bashi da muka karba maka. Domin gwamnatin tarayya ba ta ba mu damar mu karbi ko kwabo ba daga wajen wadanda suka kawo mana kara.

GTK: Daga lokacin da ka zo wannan hukuma zuwa yanzu a takaice kararraki  nawa ne kuka samu a wannan hukuma a Filato kuma  nawa ne suka sami nasara?

Abdullahi Musa: A takaice daga lokacin da na zo wannan hukuma shekaru biyu da suka gabata zuwa yanzu, mun sami kararraki guda 522, kuma a cikin wadannan kararraki mun daidai guda 237. A cikin wadannan kararki da muka daidaita akwai karar ma’aikata da suka kawo kan kudaden da suke bi bashi a ma’aikataunsu, akwai ‘yan fansho.

Mun je mun yi bincike a wuraren da suke aiki mun tabbatar haka ne kuma mun sanya an biya su hakkokinsu. Akwai wadanda suke bin wasu bashi mun kirawo wadanda ake karar mun sanya an biya su kudadensu. Haka kuma akwai ma’aikatan da aka kora a wuraren aikinsu ba bisa ka’ida ba, su ma mun sanya an mayar da su wuraren ayyukansu.  A bangaren kamfanoni nan ma mun tsaya wajen ganin sun biya ma’aikatansu da suka kawo kara kan hakkokinsu.

GTK: Idan kuka gagara sasanta wasu kararrakin kukan kai ga zuwa kotu ko kuwa yaya kuke yi?

Abdullahi Musa: Akwai wadanda idan mun buga muka ga abin ya gagara mukan kai kotu, kuma muna tsayawa mu bayar da sheda. Kuma idan mutum ya kawo mana kara, bayan ya kai kotu idan muka bincika, muka gano haka muna janyewa domin ba ma shiga maganar da aka riga aka kai kotu. Ko kuma idan wata kara tana gaban gwamna bama shiga. Amma idan aka gama wannan magana mutum ya ga abin bai yi masa dadi ba, zai iya kawo mana maganar. Kuma za mu bi wannan magana idan muka gano cewa akwai inda aka yi kuskure, za mu nuna wajen da aka yi kuskuren. Saboda an rantsar da mu a matsayin duk abin da yake gaskiya shi ne za mu bi. Abin da ya saba gaskiya shi ne za mu nuna. Saboda haka muna tsaye kan bakanmu duk wanda ya zo wajenmu za mu tsaya kan gaskiya, idan shi ne da gaskiya za mu bi masa gaskiyarsa, idan shi ne ba shi da gaskiya za mu fada masa.

GTK: Kamar a nan jihar Filato yaya ka ga yadda al’umma suka rungumi ayyukan wannan hukuma?

Abdullahi Musa: Babu shakka al’ummar Filato sun rungumi ayyukan wannan hukuma musamman a lokacin da na zo a shekara ta 2015. Kodayake nazo na samu ana zuwa amma a gaskiya zuwa na wannan hukuma mutanen da suke zuwa sun karu. Yanzu mutanen jihar nan suna zuwa sosai da sosai saboda ganin irin karbar da muke yi masu, domin  muna bi masu kararrakin da suka kawo mana kuma muna yi masu aiki tsakani da Allah.

Misali akwai wani dan sanda ya ajiye aiki yayi shekara 12, yana bin a biya shi kudaden hakkokinsa, abin ya gagara. Amma da  ya kawo mana   cikin watanni 3   muka yi aiki Allah ya taimaka aka biya shi hakkokinsa. Wannan dan sanda ya rubuto mana takardar godiya kan wannan taimako da muka yi masa, ire iren wadannan suna da yawa.

GTK: Wannan sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar Filato, dangane da ayyukan wannan hukuma?

Abdullahi Musa: Kiran da zan yi wa al’ummar Filato musamman  wadanda ba su da karfi. Duk mutumin da ya san an danne masa hakki kuma bashi da karfin da zai iya zuwa ya yi kara a gaban kotu ko gaban ‘yan sanda ya zo wannan hukuma, za mu karbe shi hannu bibbiyu mu binciki maganarsa.

Domin wannan hukuma an kafa ta ne don ta taimaki jama’a babu ruwanmu da maganar banbanci addini ko banbancin kabila. Saboda haka muna kira ga al’ummar Filato duk wanda yake da wata damuwa ya zo nan sakatariyar gwamnatin tarayya da ke garin Jos a hawa na daya, zai same mu a ofishinmu. Kuma muna da ofisoshi a kananan hukumomin  Bassa,Mangu, Panshing, Langtang, Wase da  Shendam da ke wannan Jiha ta Filato. Duk wanda yake da damuwa zai iya zuwa wajen da ya fi kusa da shi ya gabatar da damuwarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.