TAKADDAMA A KAN JANARETA YA SANYA WANI MUTUM SASSARA MAKWABCINSA

0
188
Daga Usman Nasidi
WANI karamin yaro dan shekara 16 ya bayyana wa kotu yadda wani makwabcinsu ya hallaka mahaifinsa a Jihar Legas, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Majiyarmu ta samu lamarin cewa yaron ya shaida wa kotun cewar makwabcin nasu ya kashe babansa ne bayan mahaifin nasa ya yi korafin yadda hayakin janaretan makwabcin ya addabe shi.
Yaron mai suna Adeola ya bayyana wa kotu cewa makwabcin nasu Ibrahim Tijjani ya sassari babansa ne da adda sakamakon takaddamar da ta faru a tsakaninsu.
Adeola ya ce “Matsalar da aka samu tsakanin mahaifina da makwabcinmu ta samo asali ne lokacin da mahaifina ya ce masa ya canza wajen da ya ajiye janaretansa, saboda hayakin janaretan ya dame shi, amma ya ki, hakan ya sa mahaifina dauke na’urar, kuma ya canza masa wuri.
“ Hakan ne ya sa makwabcin da mahaifina suka fara fada, daga nan makwabcin ya dauko adda ya sassara mahaifina, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa.”
Bayan sauraron jawabin lauyoyin da ke kara da na masu kare wanda ake kara sai mai shari’an ya dage sauraron karar zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.