KANAM CE KAN GABA WAJEN NOMAN AUDUGA A FILATO-HUDU HAMIDU

0
198
Isah Ahmed, Jos

SHUGABAN karamar hukumar Kanam da ke jihar Filato Alhaji Hudu Hamidu Bale ya bayyana cewa karamar hukumar Kanam ce kan gaba wajen noman auduga a jihar Filato. Alhaji Hudu Hamidu Bale ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi, a wajen kasuwar baje koli ta Jos da take ci a halin yanzu.

Ya ce muna noman auduga mai kyau a wannan karamar hukuma, kuma  muna noman auduga batare da sanya taki ba, domin kasar Kanam  tana da taki sosai.

‘’Audugar da ba a sa mata taki, tafi tsada ko a kasashen  turai. Don haka audugar da ake nomawa a karamar hukumar Kanam za a iya fita da ita zuwa kasashen waje’’.

Ya ce akwai fadamu a wannan yanki, kuma duk abin da aka shuka a karamar hukumar yana   yi, don haka manoman wannan yanki suna noman shinkafa da gyero da waken soya da sauran kayayyakin amfanin gona.

Ya ce shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce a koma  noma da kiwo   ne domin shi ne tushen komai na arziki. Don haka ya yi kira ga al’ummar  karamar hukumar Kanam da Nijeriya gabaki daya su tashi su kama aikin noma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.