NLC Na Matsa Wa El-Rufa’i Lamba Kan Korar Malamai

0
209

Rsbo Haladu Daga Kaduna

KUSAN za a iya cewa akwai alamun ga fili ga mai doki tsakanin kungiyar kwadago ta Najeriya da gwamnatin jihar Kaduna karkashin gwamna Nasiru el-Rufa’i kan yunkurin korar malaman makarantar firamare kimanin dubu 21.
A watan da ya gabata ne dai gwamnatin jihar ta yi wa malaman jarrabawa irin ta ‘yan aji hudu na firamare.
An dai yi wa malamai fiye da 33,000 jarabawar, amma kamar yadda gwamnati ta ce, kaso biyu bisa uku na malaman ba su iya samun kashi 75 cikin 100 ba bayan da sakamakon jarabawar ya fito.
Sannan kaso 66 ba ma su iya samun abin da ake bukata ba, al’amarin da ya sa gwamnatin ta sanar da cewa za ta sallami malaman da ba su iya kai bantansu ba.
Har ila yau, gwamnatin ta sanar da cewa za ta dauki sabbin malamai 25,000 domin maye gurbin 21,000 da za ta sallama. Duk da cewa har kawo yanzu gwamnatin ba ta yi cikakken jawabi ba kan lokaci da yadda za ta kori malaman, kungiyar Kwadagon kasar ta NLC karkashin jagorancin Ayuba Wabba, ta ce ba za ta sabu ba.
A ranar Laraba ne kungiyar bisa hadin gwiwar reshenta na jihar suka gudanar da zanga-zanga domin nuna kin amincewarsu kan al’amarin.
Kungiyar ta ce idan har gwamnatin ba ta janye kudirinta na korar malamai ba to za ta sanya kafar wando daya da ita.
Sai dai kuma a ranar Laraba ne gwamna el- Rufa’i, ta kafar sadarwa ta Twitter, ya ce, masu neman aikin malanta da suka kai takardunsu Hukumar Ilimin Firamare ta jihar sun kai 18,550. Ya kuma kara da cewa “har yanzu ana ci gaba da karbar takardun masu son shiga aikin na malanta”.
Wannan al’amari dai na shan suka daga bangarori daban-daban. Sai dai kuma gwamna Nasir el-Rufa’i ya ce yana
kan bakansa. Har ma a kafar tasa ta Twitter ya sanya hotunan wasu takardun jarabawar wasu malaman da suka fadi.
Yanzu dai za a iya cewa kallo ya koma sama tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.