HADIN KAN KASA SHI NE MANUFARMU-KUNGIYAR NRI

0
147
Jabiru A Hassan,  Daga Kano
SHUGABAN kungiyar farfado  da martabar arewa ta ” Northen Reformation Initiative”  (NRI)  Alhaji  Abubakar Adamu ya ce kungiyar ta fara wani aiki na kyautata dangantaka tsakanin dukkanin bangarorin wannan kasa  domin tabbatar da  ganin ana samun hadin kan kasa da kaunar juna don tabbatar da  zaman lafiya mai dorewa.
Ya yi wannan bayani ne cikin tattaunawarsu da wakilinmu dangane da aikin da kungiyar ta fara domin ganin Nijeiya ta ci gaba da kasancewa kasa daya kamar yadda aka santa, inda  kuma ya sanar da cewa shirye-shirye sun yi nisa domin fara aikin wayar da ka al’umma a kowane bangare ta yadda kowa zai fahimci cewa zaman Nijeriya  a dunkule shi ne abu mafi muhimmanci kamar yadda kowa ya sani.
Sannan ya bayyana cewa kungiyar za ta rika yin amfani da manyar harsuna hudu da ake da su a wannan kasa wajen gangamin wayar da kan al’umma ta yadda za a fahimci manufofin ta da makasudin kafata, inda ya sanar da cewa za a yi amfani da harshen Ingilishi wato Turanci da Yarabanci da Hausa da kuma yaren Ibo domin ganin kowane yanki na kasar nan ya fahimci abin da ake nufi da hadin kan kasa.
Alhaji Abubakar Adamu ya kuma nunar da cewa kungiyar “Northern Reformation Initiative” ba  ta siyasa ba ce kuma tana da mambobi daga dukkanin jam’iyyun kasar nan don haka ya ce  kungiya ce wadda aka kafa domin yin aikin wayar  da kan al’umma ta wannan  kasa yadda kowa zai san cewa akwai bukatar samun hadin kai da kaunar juna ta kowace fuska.
Haka kuma ya yi amfani da wannan dama wajen  yin albishir ga al’umar Nijeriya cewa kowane bangare yana da muhimmanci a kuma kowace kabila tana da gudummawar da za ta iya bayarwa wajen ganin ana zaune lafiya  bisa kwanciyar hankali da taimakon juna,  samnan  ya yi  kira ga dukkanin bangarorin kasar nan da su sani cewa Nijeriya kasa ce da Ubangiji ya hada zaman tare kuma zai yi kyau a ci gaba da mutun ta wannan tsari da Allah ya yi.
Daga karshe, Alhaji Abubakar Adamu ya yi amfani da wannan dama wajen nuna rashin amincewar kungiyar NRI  na shirin biyan wasu makudan kudade a matsayin diyyar yakin basasa ga wani bangare kadai maimakon a bai wa dukkanin bangarorin biyu da suka fafata wannan yaki tun da a cewar sa kowane bangare ya yi asarar rayuka da dukiyoyi a lokacin wannan rikici.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.