Mace Za Ta Iya Marin Mijinta Don Buhari’

0
127

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABAN jam’iyyar APC a jihar Katsina, Alhaji Shittu Sh’aibu Shittu, ya ce taba Buhari a siyasar jihar wani abu ne mai wuya, inda ya ce matar wanda ya soki Buhari za ta iya marinsa.
Alhaji Shittu ya yi wannan kalaman ne a lokacin da yake mayar da martani game da zargin da bangaren ‘yan APC akida ke yi na cewa gwmanatin APC mai mulki a jihar ta saki hanyar cika alkawuran da jam’iyyar ta dauka wa
al’ummar jihar.
A hirarsa da Ibrahim Isa, shugaban jam’iyyar APC a jihar Katsina ya ce: “Wasu mutane ne da suka sha kayi a zabe. Suna ganin suna da damar da ya kamata a ce sun samu mukamai a gwamnatin tarayya, kuma Allah bai sa an samu ba, kuma ba su mayar da al’amarinsu ga Allah ba.”
Da aka tambayi dan siyasar cewa ko akwai wani shiri da gwmamnatin ke yi na janyo mutanen jiki. Sai ya ce: “Iyakacin mukamin da Dallatu (Gwamnan Katsina) ke iya bayarwa shi ne kwamishina. An ba su kwamishinoni, an ba su SA, SA (mataimaka na musammman).” “Su kuma cikinsu akwai wadanda kila ministoci suke so, (wanda kuma) shugaban kasa ne ke bayarwa,” in ji shi.
Ya kare da cewa: “Da yake shi shugaban kasa idan ma ka taba shi, matarka ma sai ta mare ka, to sai aka ce bari a samu gajeruwar gwanda mai saurin tsallaka.”
‘Yan APC akida dai sun ce sun kaurace wa gwamnatin APC na jihar ne domin suna ganin gwamnatin ta dauko hanyar bijire wa alkawuran da jam’iyyar ta dauka ne a lokacin zabe.
Wasu daga cikin ‘yan APC akida a jihar Katsina din dai sun ce sun yi iya kokarinsu na kira ga gwmanatin jihar, amma “ta ki ta kula su.”
Alhaji Kabiru Abdullahi Murja na cikin jagororin APC akida a jihar, kuma ya shaida wa Ibrahim Isa cewa: “Ayyukan da aka yi alkawura ga al’ummar jihar Katsina, kusan ba su ake bisa ba. Muka ga in aka ci gaba da wannan muka kai
zamiya, abin da zai faru, APC ma ba za a yi ba.”
Ya kara da cewa: “Kuma in mun yi shiru, to, har ila yau mutane za su caje mu, shin wannan abin da masaniyarmu, koko da mu ake yin shi.” Jagoran dai ya ce sun fito ne saboda talakawan Katsina da mutane APC su san “ba  tsari suna don gajiyar gwamnatin,
Sai Alhaji Kabiru ya ce: “Ba maga  Kuma ba za mu daina ba. Sai mun ga yadda aka gyara wannan al’amarin,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.