JAM’IYYAR PDP  TANA KARA KARFI A NIJERIYA- MUSA SAYE

0
339
JABIRU A HASSAN,Daga Kano.
WANI jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Kano, Alhaji Musa Saye ya ce jam’iyyar tana kara karfi a fadin kasar nan ta yadda za ta iya karbe mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulkin kasa domin ci gaba da kyautata rayuwar al’umma kamar yadda manufofin ta suke.
Ya yi wannan tsokaci ne a hirar su da wakilinmu, inda ya kara da cewa yanzu jam’iyyar PDP ta zamo abar alfahari ga dukkanin ‘ya’yanta, sannan dukkanin wadanda suke cikin ta sun yarda cewa PDP ita ce jam’iyyar da ta kamata a yi bisa la’akari da kyawawan manufofin da take da su na bunkasa zamantakewar al’ummar kasa ba tare da nuna banbanci ba.
Alhaji Musa Saye ya kuma sanar da cewa dawowar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar cikin PDP  abu ne mai matukar muhimmanci ga dimokuradiyyar wannan kasa tamu, musamman ganin cewa Wazirin na Adamawa mutum ne mai kishin kasa wanda yake gwagwarmaya domin ganin kasar nan ta bunkasa ta kowane fanni.
Sannan ya jinjina wa tsohon shugaban rikon jam’iyyar ta PDP Sanata Ahmed Makarfi saboda kokarin da ya yi na raya jam’iyyar har aka gudanar da babban taron kasa inda aka zabi sabon shugaban jam’iyyar Uche Secoundo domin ya ci gaba da jan ragamar jam’iyyar, tare da fatan cewa dukanin ‘ya’yan jam’iyyar da aka yi wa laifi da su yi hakuri su zo a yi sabuwar tafiya don ciyar da kasa gaba.
Daga karshe Alhaji Musa Saye ya yi kira ga jagororin PDP na Jihar Kano da su yi abin da zai kara wa jam’iyyar martaba da karfi wajen tunkarar zaben kananan hukumomin da ake shirin gudanarwa cikin watan Fabarairun shekara mai kamawa,  inda kuma ya jaddada cewa zai ci gaba da ba da gudummawarsa ga ci gaban jam’iyyar ta PDP  domin ganin ta bunkasa sosai a karamar hukumar Bichi da kuma Jihar Kano baki daya, sannan ya yaba wa dukkanin wadanda suke da hannu wajen tabbatar da ganin an yi babban taron jam’iyyar cikin nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.