An Kashe Mutane 20 Tare Da Sace Shanu 300 A Taraba

0
128
Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki

Rabo Haladu Daga  Kaduna

SABON rikici ya barke tsakanin Fulani makiyaya da ‘yan kabilar Mambila a jihar Taraba
Akalla mutane 20 sun rasa rayukansu, yayin da aka yi awon gaba da shanu 300 sakamakon  sabon rikicin kabilanci a garin Mambila da ke karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba.
Wani da ya tsira da ransa a rikicin, Sa’adu Mogoggo ya shaida wa manema labarai cewa,
an kai wa gidansa hari, in da aka kashe ‘yan uwansa biyu tare da sace shanunsu, yayin da ya dora laifin farmakin kan wasu ‘yan tawayen Mambila.
Rahotanni na cewa, rikicin ya ki ci ya ki cinyewa an ci gaba da fama da tashin hankalin da wasu ke alakanta shi da rikicin Fulani makiyaya da ‘yan kabilar Mambila.
Abdu Gagarau, daya daga cikin mazauna yankin ya ce, matsalar ta yi yawa inda ya ce tashin hankalin, kuma ya tabbatar da mutuwar mutane akalla 20 tare da fadin cewa,
‘yan kabilar ta Mambila sun sace shanu sama da 300.
Gagarau ya ce, Mambilawa sun yi kaurin suna wajen kai wa sauran kabilu farmaki a Taraba da suka hada da Fulani. Sai dai ya bukaci gwamnati da ta gaggauta daukan matakin magance rikicin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.