Sabon Rikicin Filato: AKALLA RAYUKA 3 SUKA SALWANTA

0
176
Daga Usman Nasidi
RAHOTANNI sun nuna cewa rayuka uku ne suka salwanta a sabon rikicin da ya afku a tsakanin Fulani da matasan Irigwe na karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Rahotannin sun bayyana cewa, an tsinci gawar matasan Fulani biyu da yammacin ranar Litinin din da ta gabata daura da Rafin Bauna na garin Bassa bayan awanni kadan da tsinto gawar wani matashi na Irigwe.
Shugaban kungiyar makiyaya na Miyetti Allah reshen jihar Filato, Muhammad Nuru Abdullahi ya bayyana cewa, an harbe wani Ishaq Yusuf mai shekaru 19 yayin da aka tsinto gawar wani Abubakar Shehu mai shekaru 22 bayan an binne sa a wani tsukukun rami.
Yake cewa maharan sun kuma salwantar da rayukan shanu 31 tare da raunata takwas.
Babban ma’aikacin dakaru mai hulda da manema labarai, Manjo Adam Umar, shi ne ya bayar da rahoto na tabbacin wannan kashe-kashe, inda ya  ce an ci gaba da kulawa da wadanda suka raunata a gadajen asibiti.
Majiyamu ta samu labarin cewa, a ranar talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar Ghana domin taya murnar cikar ta shekaru 61 da samun ‘yancin kai.

  • ,
  • or

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.