Uwargidan Shugaban Kasa Ta Nemi A Dauki Mataki Kan Tarin Fuka

0
117

Daga Zubair Abdullahi

UWARGIDAN shugaban kasa, Hajiya A’isha Muhammadu Buhari ta yi kira da a dauki mataki kwakkwara domin a kawo karshen cutar tarin fuka TB a Najeriya da sauran kasashe makwabta.

Ta yi wannan kira ne jiya Alhamis a lokaacin da ta karbi tawagar shugabannin kungiyar tsayar da cutar TB a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Uwargida A’isha Buhari sai ta yi kira da a tashi tsaye domin a fadakar da al’umma don a tsayar da wannan cutar ta tarin fuka.Ta ce TB ana maganinsa kuma yana warkewa,kuma maganinsa kyauta ne a Najeriya. Don haka ne ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan dama su je a gwada su musamman ma idan sun dade suna fama da tari.

Uwargida A’isha ta yi alkawari za ta hada taron matan Gwamnonin Najeriya domin ta sanar da su matsalolin tarin fuka, domin su ma su je jihohinsu da kananan hukumominsu su fadakar da jama’a. Haka ma za ta yi da mata matan shugabannin kasashe makwabtanmu.

Tun farko, shugaban tawagar tsayar da TB, Dokta Suhe Savunand ya gode wa Uwargida A’isha ne ganin yadda take shugabantar wannan kamfe na tsayar da tarin uka (TB ). Taron ya sami halartar Uwargidan mataimakin shugaban kasa, Misis Dolapo Osinbajo da Uwargidan Gwamnan Jihar Nasarawa, Dokta Mairo Almakura.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.