KYAUTATA ALBASHIN MA’AIKATA ZAI KAWO INGANTUWAR AIKI  DA CI GABAN KASA-INJI ALHAJI USMAN DAN GWARI.

0
98
WANI fitaccen mai sana’ar gwari da ke Jihar Kano Alhaji Usman Dan Gwari ya bukaci gwamnatin tarayya dana jihohi da su kyautata albashin ma’aikatan su ta yadda  za a sami ingantuwar aiki da kuma ci gaba a kasar nan.
Ya yi wannan tsokaci ne a wata hira da suka yi da wakilinmu, inda ya nunar da cewa idan aka inganta albashin ma’aikata a matakai daban-daban, ko shakka babu kasar nan za ta cimma nasarorin da ake bukata musamman ta fuskar yaki da cin hanci da kuma almundahana da dukiyar al’umar kasa a fannoni daban-daban.
Alhaji Usman Dan Gwari ya kuma bayyana cewa ma’aikatan kasar nan suna bukatar kulawa ta musamman duba da yadda rayuwar al’uma take tafiya sakamakon halin matsin tattalin arziki da ake fama da shi, wanda a cewar sa, karancin albashi yana taimakawa wajen yawaitar cin hanci da satar dukiyar kasa duk kuwa da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na yaki da cin hanci.
Sannan ya yi amfani da wannan dama wajen jinjinawa ma’aikatan kasar nan saboda juriya da hakurin da suke nunawa duk da cewa albashin su ba shida inganci amma suke aikin don kishin kasa a kowane mataki, tare da fatan cewa gwamnatoci za su duba hakkin ma’aikatan su domin biyan su albashi mai kyau kamar yadda ake gani a kasashen da suka ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.