KWAMANDAN FRSC YA GARGADI  DIREBOBI DA MASU ABABEN HAWA DA KE HANYAR KANO ZUWA KATSINA.

0
137

Jabiru A Hassn, Daga Kano.

KWAMANDAN hukumar kiyaye hadurra ta kasa shiyyar Bichi Mista Yakubu Z. Lar ya gargadi direbobin motoci da sauran masu ababen hawa da ke bin hanyar Kano zuwa Katsina da su rika lura da aikin da ake yi na tagwayen hanyoyi  a wannan hanya domin ganin ana samun raguwar hadurra yayin aikin.

Ya yi wannan gargadin ne lokacin da ya duba yadda aikin cike ramukan da ke kan tsohon titin Kano zuwa Katsina yake tafiya, inda kuma ya nunar da cewa idan ana aikin gyaran hanya ko yin sabuwa ya kamata direbobi da sauran masu ababen hawa su rika lura da hanyar saboda aikin da ake yi da kuma giftawar manyan motocin aiki.

Sannan ya bukaci direbobin da su daina tukin ganganci ko gudu da al’uma ko kuma mugun lodi saboda tabbatar da cewa ana samun raguwar hadurra da kiyaye rayuka da dukiyoyin jama’a lokacin yin tafiye-tafiye walau na kusa ko kuma nesa.

Mista  Yakubu Lar ya kuma yi amfani da wannan dama wajen isar da godiyar hukumar ta FRSC ga kamfanin da ke aikin tagwayen hanyoyi  daga Kano zuwa Katsina watau CCECC saboda managrcin aiki da suke gudanarwa musamman cike dukkanin ramukan da ke kan tsohon titin Kano zuwa Katsina, wanda a cewarsa, hakan ya taimaka sosai wajen raguwar munanan hadurra kan wannan hanya.

A karshe, kwamandan shiyyar ta Bichi Mista Yakubu Z. Lar ya jinjina wa jami’ansa bisa kokarin da suke yi wajen tabbatar da ganin masu ababen hawa da ke wannan hanya suna bin dokokin tuki da kuma bin ka’idojin lodi kamar yadda ake bukata, tare da jaddada cewa za su ci gaba da aiki domin ganin al’amura suna tafiya cikin nasara da fahimtar juna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.