SULE LAMIDO YA RAGARGAJI JAMIYYAR APC A KALABA

0
151
 MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
TSOHON gwamnan jihar Jigawa dan takarar mukamin shugaban kasa karkashin  jamiyyar PDP Alhaji Sule Lamido ya yi zargin Najeriya ta fada hannun wadanda ba su da masaniyar makamar mulki koma sanin yadda ake yinsa .
Alhaji Lamido ya furta haka a kalaba lokacin da ya je gabatar musu da kansa da ‘yan jam’iyyarsu aniyarsa ta neman mukamin  shugaban kasa zaben 2019 idan Buwayi ya yi nufinmu da gani.
Ya ce “in banda rashin fasaha irin na APC ayyukan da take yin kuri da tutuya tana yi wa ‘yan Najeriya nai duk tana bin tsarin da PDP ta ajiye ne shekarun baya take son yi wa ‘yan kasar nan don haka duk gyauron abin da muka bari ne take bi.”.inji shi. Da ya juya kan tsaro kuma tsohon gwamnan Jigawa ya ce “gwamnatin APC babu abin da ta tsinana ta gaza
a wajen samar da tsaro ta kasa shawo kan matsalar Boko-Haram ta bar ‘yan Najeriya cikin yunwa haram matsala wadda take gagaruma na rashin wadata kasa da abinci”.Ya ce idan har jam’iyyar PDP ta amince masa ya yi takara babu shakka zai hada kan ‘yan Nijeriya zai magance matsalar tsaro “idan da tsaron da muke cewa sun magance shi a zo a sace ‘yan mata110 na makarantar Dapchi idan har na samu goyon bayanku shekara ta 2019 kuka rakani Aso Rock matsayin shugaban kasa ko kokwanto babu zan share hawayen ‘yan Najeriya ,gwamnatin APC ta ce za ta ba matasa ayyukan yi ga shi ta kasa ta ma rasa inda za ta bullo ma jama’a duk ta daburce”inji shi.
Karshe ya gana da magoya bayan jam’iyyarsu a ofishin jam.iyyar na Kalaba .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.