Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda A Kaduna

0
478

WATA tawagar sojojin da ke aikin zagayawa domin tabbatar da tsaron dukiya da lafiyar jama’a sun samu nasarar kama wadansu batagari su uku a garin Rijana da ke karamar hukumar Chukun a ranar 11 ga watan Afrilu 2018.

Sakamakon hakan ake kira ga jama’a da su ci gaba da hada kai da jami’an tsaro ta hanyar bayyana duk wani mai aikin nakasa tsaro domin kawo dauki cikin gaggawa.

Kamar dai yadda sanarwar ta bayyana ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin da dukkan ayyukan batagari a yankin.

Sanarwar ta bukaci a ci gaba da yin wannan sanarwa domin amfanin jama’a su san halin da ake ciki kamar yadda Birgediya Janar Texas Chukwu wanda shi ne Daraktan sashin hulda da jama’a na sojan Nijeriya ya bukata.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.