Hukumar NDLEA Ta Lalata Kwayoyi Ton 14,360 A Adamawa

0
140
NDLEA na kona miyagun kwayoyin da suka kama

Saleh Shafi’u, Daga Yola

HUKUMAR hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ta lalata haramtattun miyagun kwayoyi kimanin ton dubu goma sha hudu da dari uku da sittin (14, 360), a jihar Adamawa.

Da yake jawabi a lokacin bukin kone kayayyakin shugaban hukumar a jihar Yakubu Kibo, ya tabbatar da haka lokacin lalata kayan a gaban jama’a, ya ce an kone taron kayan miyagun kwayoyin ne bisa umurnin shugaban hukumar na kasa.

“a yau na tsaya a gabanku ina mai shaida muku muna da ton dubu 14,360 na haramtattun miyagun kwayoyi, da muka kame su daga watan Mayun 2015 zuwa Satumba 2017. “Haramtattun miyagun kwayoyin sun hada da wiwi ‘yar waje, Cough Syrup da taramol, kafsul, hodar iblis da dai sauran kwayoyi” inji Kibo.

Shugaban hukumar ya kuma kiyasta kudaden miyagun kwayoyin da cewa ya haura Naira Miliyan biyar, idan da an samu shigar da su kasuwa.

Ya ci gaba da cewa a wannan dan lokaci kawai jami’an hukumar sun kame mutum sama da dari biyar wadanda take zargi da ta’amuli da miyagun kwayoyi, ya ce dari biyu da talatin da shida daga cikin adadin tuni an tura su gudajen yari daban-daban.

“Kari a kan haka, mun kame motoci biyu, da wani gidan da ba a gama aikinsa ba, mallakar wani hamshakin dillin kwaya, mun mika su ga gwamnatin tarayya” inji Kibo.

Da shi ma yake jawabi a taron mataimakin Gwamnan jihar Martins Babale, ya yaba da kokarin hukumar a jihar, ya ce gwamnatin jihar za ta ba da hadin kai da goyon baya domin kawo karshen matsalar shan miyagun kwayoyi a jihar.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.