GUNDUMAR RIGASA TA SHUGABA BUHARI CE – Inji Gwamna El-Rufa’i

0
397
Daga Usman Nasidi Kaduna
GWAMNAN Jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i  ya yaba da irin kyautar girmamawa da wata kungiyar Azama da Wayar da kan Al’umma wato (Rigasa Action And Awareness Forum RAAF) suka ba shi a ranar Litinin din da ta gabata.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron bada kyautar girmamawa  da kungiyar ta RAAF ta gudanar a filin makarantar sakandare na gwamnati dake Titin Makarfi a garin Rigasa wanda ya gudanar domin girmama wasu al’ummar gundumar da suke tallafa wa yankin.
A cewarsa, aikin bunkasa gundumar ta Rigasa da al’ummarta wani nauyi ne wanda Shugaba Buhari ya umarce shi da ya yi domin inganta yankin a sakamakon jajircewar su wajen ganin gwamnatin APC ta cimma dukkan manufofinta a Jihar da kasa baki daya.
Ya ce “ garin Rigasa, garin Shugaban Buhari ne don haka ya ba ni umarnin kada na koma garin Abuja na ba shi wani labari ba tare da an yi wa gundumar Rigasa ingantattun ayyuka ba, shi ya sa muka sa wadannan abubuwan a gaba kuma idan Allah ya yarda duk wasu abubuwan da kuke bukata za mu yi, musamman don mu tabbatar da mutanen Rigasa ba su zama marayu ba a garin Kaduna.”
Hakazalika, ya kara da cewa wannan kyauta da aka ba da, ba shi ko gwamnatin Jihar Kaduna aka ba ba, illa gwamnati shugaban Buhari ta APC aka ba, wanda hakan ya sanya dole idan ya je garin Abuja zai sanar da shugaba Buhari wannan kyauta ta girmamawa da  aka ba shi da gwamnatinsu ta APC daga al’ummar garin Rigasa.
Gwamna El-Rufa’i, ya kara da cewa a halin da ake ciki yanzu duk wani aikin da ya fi karfin gwamnatin Jahar kaduna,to babu makawa gwamnatin Shugaba Buhari za su tabbatar da sun kammala shi, domin sun tabbata a yanzu talakawa na tare da gwamnatin APC su kuma suna goyon bayansu dari bisa dari.
A karshe, Malam Nasiru ya gode wa al’ummar Jihar Kaduna bisa ga zaben da aka yi na kananan hukumomi wanda ya gudana ba tare da an samu wani tashin hankali ko kashe-kashe ba, duk da yake an samu magudi a wasu wurare wanda hakan ya sanya ba a bayyana duka sakamakon zaben da wuri ba, kana za a sake zaben a wasu wuraren da ke kananan hukumomi da aka samu matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.