WATA BABBAR MOTA A GADAR ZARIYA TA HALLAKA AKALLA MUTANE 10

0
103
Daga Usman Nasidi

RAHOTANNI sun tabbatar da mutuwar mutane 10 a wata tashar mota mai cunkoson mutane a garin Zariya bayan wata babbar motar tirela ta kwace daga hannun direba ta kutsa cikin tashar.

Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewar babbar motar ta tattake mutanen ne bayan ta kutsa kai cikin tashar yayin da ta kwace daga hannun direban ta.

Hukumar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar hatsarin da ta ce ya faru ne ranar Lahadi da daddare, sai dai hukumar ba ta bayyana adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin ba.

Lamarin ya faru ne a kan gadar garin Zariya, a hanyar zuwa Kano, wurin da jama’a suka mayar tasha ta karfi da yaji duk da kokarin da hukumomi suka yi na ganin cewar tashar ta tashi daga wurin.

Jama’a a Najeriya na yawan korafin cewar yawancin manyan motoci ba su da wadataccen birki. Dalilin da ya sa ake samun asarar rayuka duk lokacin da birkin babbar mota ya kasa tsayar da ita.

Ana fargabar cewar adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin kan iya karuwa daga 10 da aka bayyana da farko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.