Ya Mika Wa Musulmai Sakon Fara Azumin Ramadana

0
103
Gwamna Aminu Bello Masari
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
GWAMNAN Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya Mika Sakon taya Musulmi murnar fara Azumin watan Ramadana inda ya shawarce su a kan a ci gaba da yi wa kasa addu’ar samun nasara.
Gwamna Masari ya yi wannan bayanin ne a cikin wata takardar da mai taimaka Masa a kan harkokin yada labarai Alhaji Abdu Labaran Malumfashi, ya sanya wa hannu aka rabawa manema labarai
GWAMNAN Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya yi kira ga daukacin Musulmin Nijeriya da su yi amfani da wannan watan na Ramadana a yi wa kasa tare da shugabannin ta addu’ar samun nasara. Inda Gwamnan ya kara ankarar da jama’a cewa Babu wani lokacin da ya fi na yanzu da za a dukufa wajen bautar ubangiji kamar wannan lokacin, kuma babu wani lokacin da jama’a za su sadaukar ga kasarsu kamar yanzu, musamman ganin irin yadda matsalar tsaro ke yi wa hadin Kai da zaman tare barazana.
“A matsayin wannan lokacin na bautar ubangiji, yana da kyau muyi amfani da wannan lokaci na bauta mu kara kokarin daukaka addini ba rarrabuwar Kai ba a kasa”.
“Kuma hakan zai samu ne idan mun yi amfani da koyarwar watan Ramadana, musamman nuna kauna da sayayya a tsakanin juna ba tare da nuna bambancin addini ba, taimakawa mabukata tare da nuna kishin kasa fiye da bukatun dai dai kun mutane.
“Ya kamata mu ci gaba da tunawa cewa kasa na ci gaba ne tare da duba irin kyakkyawar shugabancin ta, don haka kada mu rika koda danganta wasu abubuwa marasa kyau ga shugabanni da kasar baki daya”.
Gwamna Masari ya kara jaddada cewa Gwamnatin APC a matakin kasa da jihohi duk sun dukufa wajen ganin sun samar da shugabanci nagari da zai fitar da kasar daga cikin kalubalen cin hanci da rashawa da kuma na matsalar tsaro, Wanda Masarin ya ce duk matsalolin sun fari ne sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci a can baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.