Lalaci: YA LAKADA WA MATARSA KASHI A KAN GAZA CIYAR DA SHI

0
70

Daga Usman Nasidi

AN gurfanar da wani cima zaunen magidanci mai shekaru 47, Olakunle Adebayo a gaban kotun majistare da ke Legas bisa zarginsa da zanne matarsa da belt.Ana tuhumarsa da laifuka guda biyu wanda suke da alaka da zalunci.

Dan sanda mai shigar da kara, Saja Friday Mameh ya shaidawa kotu cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Mayun 2018 misalin karfe 7.30 ma yamma a gida mai lamba 16 layin Ikota a Lekki legas.

Ya ci gaba da cewa wanda ake zargin ya zane matarsa mai suna Misis Tolulope Adebayo ta hanyar dukkanta da belt a kai.

Mai shigar da karar kuma ta fadi ta sami rauni yayin da wanda ake tuhumar ya tunkude ta,” inji shi.

Mameh ya ce wanda ake tuhuma ya saba dukan matarsa saboda ta gaza ciyar da shi da samar da sauran bukatunsa.

Mai shigar da karar ya ce wadannan laifukan da ake tuhumar Adebayo da shi sun ci karo da sashi na 170 da 171 na dokar masu laifi na jihar Legas 2015.Sai dai wanda ake zargin ya ce bai aikata laifukan da aka karanto masa ba.

Alkalin kotun, Mista. B.I. Bakare ya bayar da belin wanda ake zargin a kan kudi N150,000 tare da mutane biyu da suka tsaya masa.

Ya ce masu tsaya masa sai sun kasance masu sana’a kuma su gabatar da shaidar biyan haraji ga gwamnatin Jihar Legas.

Alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Yuli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.