Yau Ne Gidan Rediyon Nagarta Zai Gudanar Da Ruguntsumin Sallah

0
98
Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na Jihar Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

HUKUMAR gudanarwar rediyon Nagarta Muryar hada kan jama’a karkashin jagorancin shugabanta Malam Abdulmalik Ady, sun bayyana cewa sun shirya tsaf domin gudanar da harkar wasan Ruguntsumin sallah a harabar gidan rediyon da ke Katabu a marabar Jos Kaduna.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin wanda zai jagoranci shirin Malam Jibrin Ibrahim Goma, inda ya ce sun shirya gudanar da wasan Ruguntsumin sallar ne a tsarin yin  wasanni guda uku.

Goma, ya ce a ranar washe garin sallah ne da kuma washe garin washe garin sallar ne za a yi wannan ruguntsumi na kwanaki biyu duk da misalin karfe biyu na rana zuwa shida na yammar kowace rana.

Za kuma ayi wasanni ne  irin na damben gargajiya da kuma na wakokin gargajiya da kuma na zamani.

Za dai a gudanar da wannan wasanni ne domin nishadantar da jama’a da kuma kara inganta zumunci da zaman tare.

Ana tabbatar wa da jama’a cewa za a yi wannan ne cikin tsari tare da tsaron lafiya da dukiyar jama’a, sai kun zo jama’a.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.