YADDA JIHAR FILATO TA SAKE FADAWA CIKIN RIKICI

0
216
I G Na 'Yan Sandan Najeriya

Isah Ahmed, Jos

JIHAR Filato da tayi suna wajen rikice rikicen addini da kabilanci  a shekarun baya. A ‘yan kwanakin nan  ta sake fadawa cikin wani rikicin da ya yi sanadin asarar rayukan mutane 86,   tare da raunata wasu da dama da kona gidaje da motoci da sauran dukiyoyi masu tarin yawa,  a makon daya gabata, kamar yadda hukumomin tsaro a jihar  suka bayyana.

Amma wasu majiyoyi a jihar,  sun bayyana cewa mutanen da suka rasa rayukansu a wannan rikici,  sun haura yawan adadin da hukumomin suka bayyana.

Shi dai wannan rikici kamar yadda bayanai suka nuna, ya samo asali ne sakamakon wani harin da wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne suka  kai a kauyukan Razat,Ruku,Nyarr,Kura da Gana-Ropp da ke gundumar   Gashish a  karamar hukumar Barikin Ladi, a ranar asabar din da ta gabata.

Amma wata  majiya kuma ta bayyana cewa wannan rikici ya taso ne sakamakon  tare  wasu Fulani matafiya a mota  su  5  aka yi masu kisan gilla,  a kauyen Heipang da ke karamar hukumar ta Barikin Ladi a daren ranar alhamin din makon da ya gabata ne, ya kawo tashin wannan rikici.

Rundunar ‘yan sandan jihar, ta bayyana cewa mutane 86 ne suka rasa rayukansu a wannan hari da aka kai, a yankin na Barikin Ladi. Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Terna Tyopev da ya sanya hanu aka rabawa ‘’yan jarida.

ASP Tyopev ya yi bayanin cewa bayan wannan harin da aka kai, yankin na Barikin Ladi Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Undie Adie ya tura karin rundunar ‘yan sanda ta musamman, karqashin jagorancin ACP Edeh John  zuwa yankin.

Ya ce  a binciken da rundunar ta yi a wadannan kauyuka da aka kai harin an gano gawarwakin mutane 86 da suka rasa rayukansu da mutum 6 da aka jiwa raunuka da gidaje 50 da motoci 2 da Babura 15  da aka kona a lokacin da aka kawo wannan hari.

Wannan rikici ya yadu zuwa kananan hukumomin Riyom da Jos ta Kudu. Ganin yadda wannan rikici ya yadu zuwa wadannan kananan hukumomi, ya sanya gwamnatin jihar ta sanya dokar takaita zirga-zarga daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe, a kananan hukumomin  Barikin Ladi da Riyom da Jos Kudu.

Amma duk da wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka,  wannan rikici ya cigaba da yaduwa, ya koma ramuwar gayya inda wasu matasan kabilar birom suka fito suka rika tare motocin matafiya, suna fito da mutane suna kashewa.

Wani mazaunin garin Bukur da ke karamar hukumar Jos ta Kudu, Alhaji Bala Muhammad ya shedawa  wakilinmu cewa  suna shirin fita zuwa harkokinsu, na yau da kullum  da misalin karfe 11 na safiyar ranar lahadi. Sai suka sami labarin cewa matasan kabilar birom sun tare hanyoyin shigowa ta ko’ina  a wannan gari suna fitar da mutanen  da suka ga sun yi kama da Fulani ko hausawa daga motoci suna kashewa suna konewa tare da motocin. Musamman wadanda suka fito daga taron jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja. Kamar mutanen jihohin Bauchi da Gombe da Adamawa da Yobe da Barno.

Ya ce wadannan matasa sun ci gaba da wannan  aika aika a mararrabar Jama’a da Angle ‘D’ da ke kan babbar hanyar Jos zuwa Abuja  da kuma marabar Zawan da farar Lamba da Haifan. Har ya zuwa lokacin da jami’an  tsaro suka iso da misalin karfe 5 na yammacin wannan rana,  suka tarwatsa su.

 ‘’Wadannan matasa sun yi ta yunkurin  shigowa  cikin garin Bukur, amma jami’an tsaro suka hana su. Kuma sun kashe mutane da dama cikin wadanda suka kashe har da wani babban jami’in ‘yan sanda, mai mukamin ASP’’.

 Har’ila yau wata majiya ta tabbatarwa da wakilinmu cewa a wannan hari da wadannan matasa suka kai, sun kashe wasu matasa ‘yan agajin kungiyar Izala reshen jihar Filato  Zaharadeen Sufi da Ustaz Sha’aban Kasuwan Ali, a kan hanyarsu ta zuwa garin Mangu a wannan rana.

Hakazalika  wata majiya ta tabbatarwa da wakilinmu cewa wannan al’amari ya rutsa  shugaban kungiyar Izala reshen jihar Filato kuma sakataren kudi na jam’iyyar APC reshen jihar Ustaz Ibrahim Barikin Ladi, a inda suka kona motarsa. Amma Allah yasa ya tsira da ransa.

Wata majiya ta tabbatarwa da wakilinmu cewa hatta tawagar gwamnan jihar Simon Lalong da ya fito daga Abuja wajen taron jam’iyyar APC, don ganin yazo ya kwantar da wannan rikici, sai da wadannan matasa suka farfasa wasu daga cikin motocin tawagar.

Tuni jami’an tsaro suka tabbatar da cewa an shawo kan wannan rikici, bayan tura rundunonin jami’an tsaro zuwa wuraren da rikicin ya shafa da kuma shirya tarurruka da shugabannin al’ummomin da wannan rikici ya shafa.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya nuna takaicinsa kan tashin wannan rikici da kuma irin asarar rayukan da aka yi a rikicin.

Ya mika sakon ta’aziyarsa tare da jaje ga dukkan iyalan wadanda wannan rikici ya shafa.

Ya bada tabbacin cewa gwamnati zata yi iyakar kokarinta, wajen ganin ta kamo wadanda suke da hanu kan wannan rikici domin ganin an hukumta su.

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.