YA NEMI GWAMNATI TA BAI WA HANYAR JOS ZUWA ABUJA KYAKYAWAN TSARO-DOKTA BANINGE  

0
58
Dokta Ibrahim Baninge.

Isah Ahmed, Jos

WANI mai maganin gargajiya da ke zaune a garin Jos babban birnin jihar Filato kuma Sarkin maganin masarautar Ningi, Dokta Ibrahim Baninge ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da kyakyawan tsaro,  kan babbar hanyar Jos babban birnin tarayya Abuja. Don magance irin ta’addancin da ake yiwa matafiya, a kan wannan hanya a duk lokacin da wani rikici ya tashi. Dokta Ibrahim Baninge ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, kan rikicin da ya faru a jihar Filato a ‘yan kwanakin nan.

Ya ce a lokacin da wannan rikici na jihar Filato ya tashi, an zo tare wannan  babbar hanya da  ta hada jihohi 6  da suke yankin arewacin kasar nan, aka rika yiwa matafiya wadanda basu san hawa ba basu san sauka ba, kisan gilla.

Ya ce ya kamata gwamnati ta bai wa wannan hanya cikakken tsaro don magance irin ta’addancin da ake yiwa matafi a duk lokacin da wani rikici ya tashi.

Dokta Baninge ya yi bayanin cewa sam bai kamata gwamnati ta bari a cigaba da aikata irin wannan aika aika ba, domin an dade ana yiwa matafiya ta’addanci a wannan hanya.

Ya ce abin da aka yi na kashe mutane a wannan hanya, da farwa tawagar gwamna a wannan hanya, da zanga zangar da aka yi zuwa gidan gwamnatin jihar Filato, abin takaici ne.

‘’Gwamnati ta yi adalci kan wannan rikici, domin yin adalci ga wadanda aka samu da hannu a wannan rikici, shi ne zai magance sake faruwarsa a nan gaba’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.