‘YAN SIYASA NE SUKA HADA RIKICIN FILATO-PASALI  

0
128
Alhaji Danladi Garba Pasali

Isah  Ahmed, Jos

SHUGABAN kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari ta Buhari Campaing Organisation Alhaji Danladi Garba Pasali ya bayyana cewa ‘yan siyasa  musamman  wadanda suka sace kudaden Nijeriya ne suka hada rikicin da aka yi a makon da ya gabata a jihar Filato. Alhaji Danladi Garba Pasali ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce dama an dade ana samun damuwa tsakanin Fulani makiyaya da ‘yan kabilar birom, a jihar Filato. Kuma  babu irin rikicin da ba a gani ba a jihar  zamanin gwamnatin jam’iyyar PDP. Hatta kungiyar kare haqqin dan adam ta Human Rights Watch, sun ce an rasa rayuka fiye da mutum dubu 15 a jihar Filato,  zamanin gwamnatin jam’iyyar PDP. Don haka dama wannan damuwa tana nan a kasa.

Ya ce amma da Allah ya kawo  gwamnan jihar  Simon  Lalong,  ya jawo dukkan al’ummar jihar ya hada su a wuri daya, yau shekara uku ke nan, ana zaune lafiya  a jihar.

Alhaji Danladi Pasali ya yi bayanin cewa  don haka wannan damuwa da ta taso a ‘yan kwanakin nan,  siyasa ce kawai. Wato ‘yan siyasa ne  da sauran barayin da suka sace kudaden kasar nan, suka hada wannan rikici. Domin sun ga babu abin da za su gaya wa mutanen Nijeriya.

Ya yi  tur da wannan rikici  da ya faru  kuma ya yi kira  ga  gwamnati ta dauki tsatsuran mataki, kan duk wanda aka samu da hanu kan tada wannan rikici.

 ‘’A yi bincike na musamman kan wannan rikici, babu shakka idan aka yi bincike za a gano hanun wasu ‘yan siyasa wajen tada wannan rikici. Tun da gwamna Lalong yazo an manta da maganar fadace fadace a jihar Filato. Kafin zuwan gwamna Lalong akwai wuraren da musulmi basa shiga a jihar, haka kuma akwai wuraren da kiristoci  ba basa iya shiga. Amma tun da  Lalong yazo ya hada kan al’ummar jihar, wadannan abubuwa suka zamo tarihi. Don haka bakin cikin wannan hadin kan da aka samu, ya sanya suka hada wannan rikici’’.

Ya ce wadannan mutane ba zasu sami nasara ba, domin mutanen Nijeriya, sun gane cewa saboda zabe yazo ne yasa suke kawo fitina a jihar Filato da sauran wasu sassan Nijeriya.

Ya yi   kira ga al’ummar jihar Filato,  su cigaba da zaman lafiyar da aka samu a jihar, su guji yarda wadannan ibilisai suna kawo fitina a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.