Akwai ‘Yan Gudun Hijira 34, 000 Na Kasar Kamaru A Kuros Riba – SEMA

0
111
Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki
Daga Usman Nasidi

A ranar Juma’ar da ta gabata ne cibiyar bayar da agaji na gaggawa reshen jihar Kuros Riba ta bayyana cewa, akwai kimanin ‘yan gudun hijira 34, 000 daga kasar Kamaru da ke fake cikin kananan hukumomi shida a fadin jihar.

Shugaban hukumar John Inaku, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a babban birnin Calabar na jihar.

Mista Inaku ya bayyana cewa, musabbabin da ya haifar da wannan matsala shine rikici da tashin tashina dake afkuwa a kasar sakamakon neman kamfa jamhuriyyar Ambazonia da ‘yan kudancin kasar suka bukata.

A yayin ganawar sa da kamfanin dillancin labarai Mista Inaku ya bayyana cewa, ‘yan gudun hijirar da ke neman mafaka na zazzaune cikin kananan hukumomi shida na jihar da suka hadar da; Obudu, Boki, Ikom, Etung, Akamkpa da kuma Obanliku.

Bincike ya nuna cewa a halin yanzu akwai ‘yan gudun hijira 34, 000 a jihar ta Kuros Riba inda tuni majalisar dinkin duniya ta yiwa 21, 000 rajista tare da hadin gwiwar hukumar gudun hijira ta kasa.

Mista Inaku ya kara da cewa, gwamnatin jihar na iyaka bakin kokarin ta wajen tallafa wa ‘yan gudun hijirar.

Hakazalika adadin su na kara hauhawa da gwamnatin za ta gaza wajen ci gaba da daukar nauyin su, inda ya nemi kungiyoyi da cibiyoyin jin kai akan su kawo nasu tallafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.