Wakilcin Sale Marke Ya Kawo Ci Gaba A Karamar Hukumar Dawakin Tofa- Al’umar Yankin.

0
116

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

AL’UMMAR karamar hukumar Dawakin Tofa sun nuna gamsuwar bisa yadda wakilin u na majalisar dokokin jihar, Alhaji Sale Ahmed Marke yake kokari wajen samar da aiyukan alheri a fadin yankin batare da nuna bambancin siyasa ko na ra’ayi ba.

Mafiya yawan mutanen da auka zanta da wakilin mu, aun bayyana Alhaji Sale Ahmed Marke a matsayin mutumin dake sauraron al’uma tareda yin kokari wajen ganin an aiwatar da waau daga cikin muhimman bukatun su batare da tsaiko ba.

Malam Usman Waddau, dake mazabar Gargari ya ce Alhaji Saleh Marke bayan aiki na gwamnati, ya kuma yi fice wajen taimakawa al’uma maza da mata wajen harkokin lafiya da karatu da kuma samar da hanyoyin dogaro dakai ba tare da gajiyawa ba.

Shima wani matashi Ahmad Abdu Yacko shakka babu dan majalisa Sale Marke samar da aiyukan alheri a dukkann mazabun dake fadin karamar hukumar Dawakin Tofa, wanda a cewarsa, titin da ya tashi daga Dungurawa zuwa garin Dawakin Tofa yana daga cikin hanyoyin da al’umar wannan yanki ke bukata ana nan ana yin sa kuma mai inganci.

Sauran wadanda suka zanta da Gaskiya Ta Fi Kwabo sun sanar da cewa nan gaba kadan zasu fara wani gangami na nuna sahihancin Alhaji Sale Marke a matsayin wakilin karamar hukumar Dawakin Tofa, tareda yin kira ga dukkanin al’umar yankin dasu ci gaba da goyon bayan wakilin nasu domin ya sake cin zabe ta yadda zai dora wajen samar masu da aiyukan raya kasa kamar yadda yake yi a halin yanzu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.