Har Yanzu Ina Nan A PDP Ban Sauya Sheka Ba – Shekarau

0
61

Daga Usman Nasidi

TSOHON gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim shekarau, ya ce shi bai sauya sheka daga PDP ba

Hadimin dan takaran kujerar shugaban kasar ne ya sanar da batun ficewar nasa –

Sai dai ya karyata hakan a shafinsa na twitter Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takaran kujerar shugaban kasa, Mallam Ibrahim shekarau, ya ce shi bai sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ba kamar yadda rahotanni ke nunawa.

A safiyar ranar Talata, 4 ga watan Satumba ne hadimin Shekarau akan kafofin watsa labarai, Sule Ya’u Sule ya sanar da rashin amincewarsu da abin da ya kira “rashin adalci” da ake masu daga hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Rahotanni da dama sun ruwaito Sule yana mai bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar bisa wannan dalili.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.