Wata Kungiya Ta shigar Da Karar ‘Yan Majalisun Da Suka Sauya Sheka

0
52

 

Daga Usman Nasidi

WATA kungiya mai wayar da kan jama’a, Enough is Enough (EiE) Nigeria, ta shigar da kara a babban kotun Abuja inda ta ke bukatar kotu da kori dukkan ‘yan majalisa da suka sauya sheka domin a gudanar da zabin maye gurabensu.

Wasu daga cikin ‘yan majalisan da suka sauya sheka sun hada da shugaban majalisa Bukola Saraki da tsohon shugaban marasa rinjaye, Godswill Akpabio.

A yayin da Saraki ya sauya sheka daga APC zuwa PDP, Akpabio ya yi kishiyar hakan. Kungiyoyi sun hada kai don kai Saraki da Akpabio kara kan sauyin sheka.

A karar da kungiyar ta shigar mai lamaba FHC/ABJ/CS/923/2018 a ranar 28 ga watan Augustan 2018, kungiyar ta ce ‘yan majalisar sun fice daga jam’iyyun da suka basu inuwar takara kuma su kayi nasara ba tare da rabuwan kai a jam’iyyar ba.

Kungiyar ta ce dan majalisa yana iya cigaba da kasancewa a kujerarsa ne bayan sauya sheka idan jam’iyyarsa ta rabu kashi biyu kamar yadda ta faru a shari’ar Abegunde da majalisar jihar Ondo a 2015.

Kungiyar kuma ta bayar da misalin abinda ya faru a majalisar jihar Kaduna inda Kakakin majalisar ya sanar da cewa za’a gudanar da zaben maye gurbin wasu ‘yan majalisa biyu da suka sauya sheka.

“Muna son a cigaba da daukan irin wannan matakin a dukkan jihohin Najeriya da babban birnin tarayya.

A halin yanzu ba’a tsayar da ranar sauraron karar ba saboda ba’a mika shari’ar ga alkalin da zai saurare ta ba.

Shugaban tsare-tsare na kungiyar, Dapo Awobekun ya bukaci a kotun tayi gagawar fara sauraron shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.