LALONG KA GYARA HANYOYIN JOS KO MUKI ZABENKA-MATASAN GARIN JOS

0
72

Isah Ahmed, Jos

HADAKAR kungiyoyin matasan garin Jos fadar gwamnatin jihar Filato, ta baiwa gwamnan jihar  Simon Lalong  sharadin ya gyara hanyoyin cikin garin Jos, da aka fara aikin gyarawa kamar yadda ya yi alkawari, ko kuma suki sake zabensa a zabe mai zuwa.

Hadakar kungiyoyin matasan  da ta kunshi kungiyoyi  19 ta baiwa gwamnan  wannan sharadi ne, a lokacin da ta kira gangamin matasan garin Jos, don gudanar da aikin gayya na cike ramukan hanyoyin cikin garin da suka lalace a karshen makon da ya gabata.

Da yake zantawa da ‘yan jarida a wajen aikin  shugaban hadakar kungiyoyin Barista Buhari Ibrahim Shehu ya bayyana cewa  gwamnatin jihar Filato ta gwamna  Lalong ta dauki hanyoyin da zata gyara a cikin garin Jos. Kamar hanyar unguwar Rogo da unguwar Rimi da hanyar kasuwar New Market da hanyar Rikkos kamar yadda tayi alkawari.

Ya ce an fara aikin gyara wadannan hanyoyi tun a shekara ta 2016, aka  tone wadannan hanyoyi gabaki daya aka yi ramuka, sai aka baraikin kusan shekaru 3 ke nan.

Barista Buhari Ibrahim Shehu ya yi bayanin cewa  wadannan hanyoyi  sun shafi kasuwanni da shaguna, baya ga dubban mutanen da suke amfani da su.

Ya ce a lokacin rani kowa yana cin wahala a cikin wannan gari, sakamakon yadda aka lalata wadannan hanyoyi, kura tana tashi da jar kasa, duk masu shaguna sai dai su rufe. Yanzu kuma da aka shiga damina hanyoyin suka kara lalacewa ruwa na taruwa  kan hanyoyin.

Ya ce don haka  suka yi rubutu suka kai ofishin gwamnan  kan  cewa azo a dauki matakin gyara wadannan hanyoyi, domin mutanen Jos suna cikin wani mawuyacin hali, saboda lalacewar wadannan hanyoyi.

Ya ce wata guda ke  nan, har yanzu babu wani bayani da aka yi. ‘’Don haka muka yanke shawarar muzo mu yi aikin gayya mu tara kudade mu sayi kasa da duwatsu  mu cike ramukan da aka haka  a wadannan hanyoyi, domin  mutane su sami sauki. Kuma muna  son ‘yan jarida su gayawa gwamnan,  lallai azo a gyara wadannan hanyoyi.Domin idan aka yi zabe ba  a gyara wadannan hanyoyi ba, ya zama  ba za a gyara ba ke nan’’.

Shugaban matasan ya ce tun da Allah yasa da kuru’unsu ne gwamnan  ya ci zaben gwamnan  Filato.  Sun  yanke shawarar idan ba a gyara wadannan hanyoyi ba, zasu dauki matakin wayar da kan jama’ar Jos cewa gwamna ya yi masu alkawari, amma ya saba kuma bashi da niyar cikawa don haka su canza su zabi wanda suke ganin zai yi, wannan aiki.

Har’ila yau ya yi kira ga shugabannin al’ummar  Jos musamman malamai su tuna cewa sune suka tsaya suka ce a zabi Simon Lalong a zaben shekara ta 2015. Don haka su gayawa masa  gaskiya cewa ba za a kara zabensa ba, matukar bai cika wannan alkawari da ya yi ba.

A lokacin da aka tuntube kwamishinan watsa labaran jihar Filato, Mista Yakubu Dati kan wannan al’amari, ya bayyana cewa tuni gwamna Lalong ya yi taro da ‘yan kwangiyar da suke aikin wadannan hanyoyi. Kuma da zarar gwamnatin jihar ta sami kudade zata baiwa wadannan ‘yan kwangila, domin su koma su cigaba da aikin gyara wadannan hanyoyi.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa babu wasu aikin hanyoyi da aka yi watsi da su a jihar. Sai dai an dakatar da aikin wasu hanyoyin ne saboda lokacin damina na ruwan sama  da ake ciki. Domin babu yadda za ayi a cigaba da aikin gyaran hanya a lokacin damina.

Ya ce tuni kwamishinan ma’aikatar ayyuka na jihar da Mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, suka ziyarci wadannan hanyoyi kuma nan bada dadewa ba za a cigaba da aikin gyara wadannan hanyoyi.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.