KU FITAR DA RAN SAMUN ALBASHI A KAN LOKACI – BABBAN AKAWUN TARAYYA GA MA’AIKATA

0
143

 

Daga Usman Nasidi

A RANAR Alhamis ne Babban Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris ya yi kira ga Hukumar Kwadago na kasa ta tsagaita yajin aikinta saboda ofishinsa ta samu damar kammala biyan albashin ma’aikata na wannan watan.

A jawabin da ya yi a Abuja, Mr idris ya ce fara yakin aikin ya janyo jami’an da ke aikin biyan albashi sun kasa samun damar shiga ofisoshinsu domin gudanar da ayyukansu na biyan albashin.

Ya ya gargadin cewa biyan alabashi ba zai yiwu a irin wannan halin ba muddin ba’a kyale masu ruwa da tsaki sun shiga ofisoshinsu ba domin biyan albashin.

Ya ce yajin aikin zai sanya gwamnatin tarayya ta kasa biyan albashi ma’aikata kafin karshen wata kamar yadda ta yi alkawari a baya.

Idris ya roki Kungiyar Kwadagon ta bawa ma’aikatansa damar shiga ofisoshinsu domin su biya ma’aikata albashin wannan watan. Ya ce shi da ma’aikatansa sun iso ofishinsu amma an hana su shiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.